2021: Gwamnatin Zamfara zata kashe N1bn kan masallatai da islamiyoyi da wasu ayyukan addini

2021: Gwamnatin Zamfara zata kashe N1bn kan masallatai da islamiyoyi da wasu ayyukan addini

- Gwamnatin Jihar Zamfara ta za ta ware wa ma'aikatar harkokin addini naira biliyan daya a kasafin kudin 2021

- Kwamishinan harkokin addini na jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ga majalisa

- Ya ce za a yi amfani da kudin ne wurin gina masallatai, isalamiyoyi, gini da gyaran makabarta, bincike da karatun addini da sauransu

Gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Kasafin kudin 2021: Gwamnatin Zamfara zata kashe N1bn kan masallatai da islamiyoyi
Kasafin kudin 2021: Gwamnatin Zamfara zata kashe N1bn kan masallatai da islamiyoyi. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mun binciko gwamnan Arewa da ke da hannu a ta'addanci a yankin, in ji APC

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

"A kasafin 2021, mun shirya gyara makarantun islamiyyun mu, gina sababbi da kuma inganta makabartu.

"Daga cikin kasafin, zamu taimaka wajen karawa malaman addini ilimi," inji Jangebe.

Shugaban hukumar shari'a da bincike, Abubakar Sodangi, ya ce hukumar zata wallafa littafan shari'ar musulunci.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya bayyana yadda ya ceto ɗaliban Ƙanƙara 344 ba tare da biyan kuɗin fansa ba

"A kasafin 2021, mun bukaci a wallafa littafan binciken shari'ar musulunci a harsuna guda hudu - Larabci, Hausa, Turanci da Fulatanci.

"Munufar shine malamai a fadin jihar su kara ilimi," a cewarsa.

Shugaban hukumar tace kira'ar Qurani, Hadi Sulaiman, ya ce hukumar zata gina makarantun musabakar Qurani a kananan hukumomi 14 da ke fadin jihar.

A cewarsa, wannan yana daga yunkurin gwamnati na kakkabe bara daga jihar.

A baya kunji wasu miyagu da ake zargin yan bindiga ne sun tare tawagar Manjo Sanusi Muhammad Asha, Sarkin Kauran Namoda a Jihar Zamfara inda suka kashe mutum takwas ciki har da yan sanda guda uku.

SaharaReporters ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a babban titin Gusau zuwa Funtua.

Majiyoyi sun ce sarkin yana kan hanyarsa zuwa hallarton wani taro ne a Gusau yayin da yan bindigan suka afka wa tawagarsa suka kashe yan sanda guda uku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164