Na yi nadamar yanka rago don murnar nasarar Buhari a 2015, in ji wani ɗan Najeriya

Na yi nadamar yanka rago don murnar nasarar Buhari a 2015, in ji wani ɗan Najeriya

- Wani ɗan Najeriya, Al Amin Yahya, ya bayyana rashin jin daɗinsa game da ƙallubalen tsaro a ƙasar

- Mutumin ya ce ya yi nadamar yin azumi da yanka rago don murnar nasarar Shugaba Buhari a 2015

- Al Amin ya bayyana hakan ne yayin martani ga hadimin shugaban kasa kan ceto ɗaliban makarantar Ƙanƙara

Wani ɗan Najeriya mai suna Al Amin Yahya ya fito fili ya ce ya yi nadamar yanka rago domin murnar nasarar da Shugaba Buhari ya samu a zaben shekarar 2015, LIB ta ruwaito.

Yahya wanda a baya ɗan gani kashe in Buhari ne ya bayyana hakan ne yayin mayar da martani kan rubutun da hadimin shugaban ƙasa, Bashir Ahmad ya yi game da ceto ɗaliban Ƙanƙara lafiya.

DUBA WANNAN: Gwamnan Zamfara ya bayyana yadda ya ceto ɗaliban Ƙanƙara 344 ba tare da biyan kuɗin fansa ba

Na yi nadamar yanka rago don murnar nasarar Buhari a 2015, in ji wani ɗan Najeriya
Na yi nadamar yanka rago don murnar nasarar Buhari a 2015, in ji wani ɗan Najeriya. Hoto daga @ElAmeen4real
Asali: Twitter

Yahya ya rubuta;

"A bangaren tsaro, ban taɓa ganin gwamnatin da ta gaza kare al'ummar ta kamar wannan ba, na yi nadamar yin azumi don Buhari ya ci zaɓe, na yi nadamar yanka rago da na yi don nasarar sa a 2015. Na yi nadamar jinkirta sallar Fajr don in kaɗa masa ƙuri'a a ranar."

Na yi nadamar yanka rago don murnar nasarar Buhari a 2015, in ji wani ɗan Najeriya
Na yi nadamar yanka rago don murnar nasarar Buhari a 2015, in ji wani ɗan Najeriya. Hoto: @Elameeen4Real
Asali: Twitter

A wani rahoton daban, gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kai wa tawagar sarkin Kauran Namoda hari, mutum takwas sun mutu

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel