Yan bindiga sun kai wa tawagar sarkin Kauran Namoda hari, mutum takwas sun mutu

Yan bindiga sun kai wa tawagar sarkin Kauran Namoda hari, mutum takwas sun mutu

- Yan bindiga sun afka wa tawagar sarkin Kauran Namoda, Manjo Sanusi Muhammad Asha

- Miyagun sun afka wa tawagar sarkin ne a hanyar Gusau zuwa Funtua inda suka kashe mutum takwas

- Cikin wadanda aka kashe akwai kawun sarki mai suna Dan Amal da kuma yan sanda uku da dogari da direba

Wasu miyagu da ake zargin yan bindiga ne sun tare tawagar Manjo Sanusi Muhammad Asha, Sarkin Kauran Namoda a Jihar Zamfara inda suka kashe mutum takwas ciki har da yan sanda guda uku.

SaharaReporters ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a babban titin Gusau zuwa Funtua.

Majiyoyi sun ce sarkin yana kan hanyarsa zuwa hallarton wani taro ne a Gusau yayin da yan bindigan suka afka wa tawagarsa suka kashe yan sanda guda uku.

Yan bindiga sun kai wa tawagar sarkin Kauran Namoda hari, mutum takwas sun mutu
Yan bindiga sun kai wa tawagar sarkin Kauran Namoda hari, mutum takwas sun mutu. Hoto: @TVCNews
Source: Twitter

Yan bindiga sun kai wa tawagar sarakin Kauran Namoda hari, mutum takwas sun mutu
Yan bindiga sun kai wa tawagar sarakin Kauran Namoda hari, mutum takwas sun mutu. Hoto: @OfficialLifeInArewa
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Mun binciko gwamnan Arewa da ke da hannu a ta'addanci a yankin, in ji APC

An kuma kashe wani direban Hilux a tawagar, da babban dogarin sarki da wani Dan Amal, wadda kawu ne ga sarkin na Kauran Namoda.

An yi kokarin kiran kakakin rundunar yan sandan jihar domin ji ta bakinsa amma bai daga wayar ba kuma bai kira ba.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya bayyana yadda ya ceto ɗaliban Ƙanƙara 344 ba tare da biyan kuɗin fansa ba

Zamfara, kamar sauran wasu jihohin Arewa yana fuskantar kallubalen tsaro inda yan bindiga da masu garkuwa ke kai wa mutane hari akai akai.

Ko baya bayan nan ma wasu yan bindigan sun sace dalibai daga makarantar kwana ta Kankara a Jihar Katsina.

Sai dai bayan yan kwanaki gwamnati da hadin gwiwar sojoji da wasu hukumomin tsaro ta ceto yaran.

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel