Gwamnan Zamfara ya bayyana yadda ya ceto ɗaliban Ƙanƙara 344 ba tare da biyan kuɗin fansa ba
- Bello Matawalle, gwamnan Zamfara ya ce shine ya shiga tsakani har ƴan bindiga suka sako ɗaliban Ƙanƙara 344
- Gwamnan ya kuma ce bai biya ko naira ɗaya ba a matsayin kudin fansa don karɓo yaran
- Kazalika, Matawalle ya ƙaryata jita-jitar cewa Boko Haram na da hannu a sace yaran inda ya ce ƴan bindiga ne
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana yadda ya saka baki aka dawo da ɗaliban makarantar sakandare ta Ƙanƙara 344 ba tare da biyan kuɗin fansa ba.
A ranar Juma'a da ta gabata ne aka sace yaran daga makarantar su da ke garin Kankara.
Duk da cewa Boko Haram ta yi ikirarin cewa itace ta sace yara 524, gwamnatin Katsina ta ce ɗalibai 344 kawai aka yi garkuwa da su.
DUBA WANNAN: Kano: Bangaren Wali ta kori Kwankwaso daga PDP har abada
A hirar da Matawalle ya yi da Daily Nigerian, ya ce ya yi amfani da tubabbun ƴan bindiga da shugabannin Miyetti Allah wurin gano wadanda suka sace yaran tare da tattaunawa da su.
"Mun tuntube su, na lallaɓa su su sako yaran kuma sun sako su a daren yau (Alhamis). Ba wannan ne karo na farko da muke karbo mutanen mu ba tare da biyan fansa ba.
"Ka tambayi kowa, ba mu biyan ƴan bindiga ko sisi. Abinda muke yi shine basu daman su tuba domin suma suna son su zauna lafiya.
KU KARANTA: Mun binciko gwamnan Arewa da ke da hannu a ta'addanci a yankin, in ji APC
"A yanzu da muke magana, suna hanyarsu ta zuwa Tsafe daga nan za su zo Gusau su kwana. Za su tafi Katsina gobe da safe," in ji gwamnan.
Gwamnan ya kuma ƙaryata jita-jitar cewa Boko Haram ne ta sace yaran. "Babu hannun Boko Haram a wannan, Ƴan bindiga ne," a cewar gwamnan.
A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.
The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.
Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng