Tsoffin shugabannin Afrika 10 da suka mutu a 2020

Tsoffin shugabannin Afrika 10 da suka mutu a 2020

- Shekarar 2020 ta zo da manyan kalubale ga mutane da dama a fadin nahiyar Afrika

- Yayinda nahiyar ke gwagwarmaya da gurbatacciyar gwamnati, an samu tsaiko a tattalin arzikinta saboda annobar korona

- Wannan shekarar ta kuma zo da mace-mace da dama na tsoffin shugabanni a nahiyar

Tsoffin shugabannin Afrika da dama sun mutu a 2020 yayinda shekarar ta kasance mai tattare da kalubale da dama ga nahiyar gaba daya.

Annobar korona ita ta kara lalata shekarar yayinda mace-mace da dama suka afku sakamakon cutar toshewar numfashin.

Legit.ng ta jero wasu tsoffins shugabannin Afrika 10 da suka mutu a 2020.

Tsoffin shugabannin Afrika 10 da suka mutu a 2020
Tsoffin shugabannin Afrika 10 da suka mutu a 2020 Hoto: @officeofJJR
Source: Twitter

1. Pierre Buyoya (Burundi)

Ya mutu a kasar Paris sakamakon cutar korona yana da shekaru 71 a duniya.

Buyoya ya kasance jagora da ya taimaka wajen samun damokradiyya a karamar kasar ta Afrika amma aka zarge shi da hannu a kisan wanda ya gaje shi a mulki.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Anambra ta tsige wasu manyan sarakuna uku

2. Pierre Nkurunziza (Burundi)

Shugaban kasar Burundi mai barin gado a wannan lokacin Pierre Nkurunziza ya mutu a kan karagar mulki jim kadan bayan zaben Shugaban kasa lokacin da magajinsa, Evariste Ndayishimiye, ke shirin karbar mulki.

An tattaro cewa ya mutu sakamakon matsala da ta shafi numfashi koda dai wasu shafukan sadarwa musamman a soshiyal midiya sun ce annobar korona ce.

3. Edem Kodjo (Togo)

Tsohon dan diflomasiyyan ya mutu yana da shekaru 82 a babbar birnin Paris a ranar 11 ga watan Afrilu.

Kodja ya shafe zango biyu a matsayin Firayim minista, na farko daga 1994 zuwa 1996 sannan kuma daga 2005 zuwa 2006 karkashin tsohon Shugaban kasa Gnassingbe Eyadema.

4. Daniel Arap Moi (Kenya)

Moi, tsohon malamin makaranta ya kasance Shugaban kasar Kenya na tsawon shekaru 24, inda ya zama shugaba mafi dadewa a kasar.

Ya kasance a asibiti tsawon fiye da wata guda a lokacin mutuwarsa.

5. Emmanuel Issoze Ngondet (Gabon)

A watan Yuni, Shugaban kasar Gabon, Ali Bongo ya wallafa labarin mutuwar tsihon Firayim minista Emmanuel Issoze-Ngondet.

Ya yi aiki a matsayin Firayim minista tsakanin 2016 da 2019 har sai da aka maye gurbinsa da Julien Nkoghe Bekale.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Usman Faruk, gwamna na farko a mulkin soja ya rasu

6. Amadou Gon Coulibaly (Côte d'Ivoire)

Amadou Gon Coulibaly ya mutu yana da shekaru 61 a babbar birnin kasar Abidjan.

Marigayin ya shafe makonni biyu ne kawai a gida bayan tafiya jinya da yayi na tsawon watanni biyu a kasar Faransa.

7. Benjamin Mkapa (Tanzania)

Ya rasu yayinda yake jinya a asibitin Dar es Salaam yana da shekaru 81.

Tsohon Shugaban wanda aka haifa a ranar 12 ga watan Nuwamba, 1938; Mkapa ya jagoranci Tanzania daga 1995 zuwa 2005 kafin ya mika mulki ga Jakaya Mrisho Kikwete.

Ya kasance Shugaban kasar ta gabashin Afrika na uku sannan ya jagoranci taruka da dama na zaman lafiya a yankin.

8. Jerry John Rawlings (Ghana)

Tsohon Shugaban kasar na Ghana ya mutu yana da shekaru 73. Ya yi kimanin zango uku a matsayin shugaba a shekarun da Ghana ta samu yanci.

Zango biyu a mulkin soja da kuma zango biyu a matsayin zababben Shugaban kasa na damokradiyya.

9. Amadou Toumani Toure (Mali)

Ya mutu yana da shekaru 72 a wani asibitin a kasar Turkiyya. Yana kan farfadowa daga wani aiki da aka yi masa a zuciya a Bamako kafin ya tabarbare, lamarin da yasa aka kwashe shi zuwa Turkiyya.

Touré ya kasance shuganan kasar Mali daga 2002 zuwa 2012 kafin sojoji suka tunkudar da mulkinsa.

10. Mamadou Tandja na Nijar

Tsohon Shugaban kasar Nijar ma ya mutu a karshen watan Nuwamba yana da shekau 82.

An sanar da mutuwar Tandja a wata sanarwa da aka yi a gidan talbijin na kasa, inda aka bayar da hutun kwanaki uku don yin alhini.

Ya lashe zabuka sau biyu bayan kasar ta dawo mulkin farar hula a 1999. Bayan shekaru sai aka tunkudar da gwamnatinsa.

A wani labarin, wasu masana a fadin kasar nan sun bayyana cewa bude iyakokin tudun Najeriya da gwamnatin tarayya ta bada umarni ayi, yana da tasiri ga tattali.

Jaridar Sahara Reporters ta ce wadannan masana harkar tattalin arziki sun ce bude iyakokin da aka yi, yana da amfani da illa ga mutanen Najeriya.

A hirar da jaridar ta rika yi da wasu masana da-dama, sun bayyana wasu daga tasirin wannan mataki a zamantakewa da halin tattalin da ake ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel