Yanzu Yanzu: Usman Faruk, gwamna na farko a mulkin soja ya rasu

Yanzu Yanzu: Usman Faruk, gwamna na farko a mulkin soja ya rasu

- Mutanen jihar Gombe sun tsinci kansu a cikin wani yanayi na alhini

- Hakan ya kasance ne sakamakon mutuwar gwamna na farko a mulkin soja a jihar ta arewa maso yamma, Alhaji Usman Faruk

- Tsohon kwamishinan yan sandan ya rasu a ranar Juma’a kuma shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana shi a matsayin jigo na gaskiya

Usman Faruk, gwamna na farko a mulkin soja a jihar arewa maso yamma, ya rasu, lamarin da ya jefa Gombe cikin halin juyayi.

Tsohon gwamnan na mulkin soja ya rasu a ranar Juma’a, 18 ga watan Disamba.

Ya yi aiki a matsayin gwamna a mulkin soja a jihar ta arewa maso yamma daga 1967 zuwa 1975 bayan an wareta daga tsohuwar yankin arewa a mulkin soja na Janar Yakubu Gowon.

Yanzu Yanzu: Usman Faruk, gwamna na farko a mulkin soja ya rasu
Yanzu Yanzu: Usman Faruk, gwamna na farko a mulkin soja ya rasu Hoto: Daily Trust/Pressreader
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Daliban Kankara: Ina neman afuwa, ku yafe min: Garba Shehu ga yan Najeriya

Da yake martani a kan mutuwarsa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana Faruk a matsayin jigo na gaskiya wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hadin kan kasar.

Buhari, wanda yayi magana a wata sanarwa daga kakakinsa, Garba Shehu, ya ce tsohon kwamishinan yan sandan ya kasance mutum mai alkhairi da tawali’u.

Jawabin ya zo kamar haka:

“Shugaban kasar ya kuma mika ta’aziyyarsa zuwa ga gwamnati da mutanen jihar Gombe, tare da cewar dansu kuma Jarman Gombe, ya sadaukar da rayuwarsa da karfinsa wajen hadin kan kasa.

“Shugaba Buhari ya kuma lura cewa Alhaji Faruk ya jajirce wajen ci gaban al’ummansa har bayan da yayi ritaya, inda ya kara da cewa marigayin ya kasance mai alheri da tawali’u.

“Yayinda aka sada tsohon jami’in dan sandan da gidansa na gaskiya a ranar Juma’a, Shugaban kasar na addu’a kan Allah ya ba dukkanin masu juyayin rasuwarsa dangana sannan ya ji kansa da rahma.”

A wani labarin na daban, masu garkuwa da mutane sun sace Shaibu Usman, Eje na Ankpa na wucin gadi a ranar Juma'a misalin karfe 5.30 na yamma a Ankpa da ke karamar hukumar Ankpa yayin da ya ke kokarin shiga masallaci.

KU KARANTA KUMA: Ba ni da wani uziri da zai hana ni samar wa Najeriya tsaro, Buhari

Majiyoyi sun shaidawa HumAngle cewa masu garkuwan sun yi da suka labe a masallacin sunyi awon gaba da basaraken nan take kuma ba a san inda suka tafi da shi ba.

A lokacin da aka hada wannan rahoton, masu garkuwan ba su tuntubi iyalansa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel