Tattalin arziki: Jerin tasirin rufe iyakokin tudu da Gwamnatin Tarayya tayi

Tattalin arziki: Jerin tasirin rufe iyakokin tudu da Gwamnatin Tarayya tayi

- A ranar Laraba, 16 ga watan Disamba, 2020, aka bude iyakokin kasan Najeriya

- Masana sun bayyana cewa rufe iyakokin ya haddasa masifaffen tashin farashi

- Da wannan mataki da aka dauka, za a koma fasa-kaurin man fetur zuwa ketare

Wasu masana a fadin kasar nan sun bayyana cewa bude iyakokin tudun Najeriya da gwamnatin tarayya ta bada umarni ayi, yana da tasiri ga tattali.

Jaridar Sahara Reporters ta ce wadannan masana harkar tattalin arziki sun ce bude iyakokin da aka yi, yana da amfani da illa ga mutanen Najeriya.

A hirar da jaridar ta rika yi da wasu masana da-dama, sun bayyana wasu daga tasirin wannan mataki a zamantakewa da halin tattalin da ake ciki.

KU KARANTA: Hankalin Duniya ya kwanta da aka ceto yaran Kankara - Buhari

1. Shigo da kaya

Farfesa Akpan Ekpo yace da bude iyakokin da aka yi a makon nan, kayan kasashen ketare za su shigo Najeriya inda za su kashe kasuwar kayan cikin gida.

2. Fasa-kaurin man fetur

A cewar Akpan Ekpo, da wannan mataki da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka, za a dawo da shiga da fetur zuwa kasashen ketare ta barayin hanyoyi.

3. Farashin kaya a kasuwa

Masanin tattalin arzikin yace kaya za su rika shiga su na fita sosai wanda hakan zai yi dalilin raguwar farashi da tsadar kaya da ake fama shi a Najeriya.

Farfesa Segun Ajibola na jami’ar Babcock, jihar Osun, yace bude iyakokin da aka yi zai taimaka wajen karya farashin kayan masarufi na wani gajeren lokaci.

KU KARANTA: Gwamnatin Kaduna za ta shigo da magungunan Coronavirus daga waje

Tattalin arziki: Jerin tasirin rufe iyakokin tudu da Gwamnatin Tarayya tayi
Ministar kudi Zainab Ahmed Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

4. Kashe kamfanonin gida

A cewar Farfesa Leo Ukpong, za a kashe ‘yan kasuwan gida tun da gwamnati ta bude iyakoki, kuma an gaza kawo manufofin da za su tada kamfanonin kasa.

Kun ji cewa watakila gwamnatin tarayya da Muhammadu Buhari ta ke jagoranta a Najeriya ta garkame layin wayoyi miliyan 161.5 nan da karshen shekara.

Sabon umarnin da hukumar NCC ta bada, ya na daf da jefa miliyoyin mutane a hadarin rasa layin wayoyinsu. An wajabtawa kowa hada layinsu da lambar NIN.

Idan ba a kara wa'adin ba, mutum 161,500,000 zasu iya wayan gari an toshe masu layin SIM.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel