Gwamnatin Anambra ta tsige wasu manyan sarakuna uku

Gwamnatin Anambra ta tsige wasu manyan sarakuna uku

- Gwamnatin Anambra ta tsige wasu manyan sarakunan jihar guda uku

- Greg Obi, kwamishinan harkokin sarauta na jihar Anambra, ya bukaci a tsigaggun sarakunan su dawo satifiket dinsu

- Sai dai daya daga cikin sarakunan da abun ya shafa, ya ce ba a sanar masa ba, inda yace lallai har yanzu shi basarake ne

Gwamnatin jihar Anambra a ranar Juma’a, 18 ga watan Disamba, ta sanar da tsige wasu sarakuna uku.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sarakunan da abun ya shafa sune Igwe Chijioke Nwankwo na Nawfia, Igwe Anthony Onyekwere na Owelle da kuma Igwe G. B. C Mbakwe na Abacha.

Legit.ng ta tattaro cewa gwamnatin jihar ta kuma janye satifiket din da ke nuni ga sarakunan.

Gwamnatin Anambra ta tsige wasu manyan sarakuna uku
Gwamnatin Anambra ta tsige wasu manyan sarakuna uku Hoto: Chief Willie Obiano
Source: Facebook

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Usman Faruk, gwamna na farko a mulkin soja ya rasu

A cewar jaridar Daily Trust, tsigaggun sarakunan na daga cikin sarakuna 12 da aka dakatar kan ziyartan Abuja domin ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba tare da amincewar gwamnatin jihar ba.

Kwamishinan kananan hukumomi, da harkokin sarauta na jihar, Greg Obi, ya umurci sarakunan da su dawo da satifiket dinsu zuwa sakatariyar yankunansu.

A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta dage dakatarwar da aka yiwa biyar daga cikin sarakunan 12 yayinda sauran uku ke karkashin tantancewa.

Da yake martani kan ci gaban, sarkin Nawfia, Igwe Chijioke Nwankwo, ya ce gwamnatin jihar bata sanar masa da lamarin ba.

KU KARANTA KUMA: 2021: Gwamnatin Zamfara zata kashe N1bn kan masallatai da islamiyoyi da wasu ayyukan addini

Ya ce:

“Muna a kotu kan wannan lamari tare da umurnin cewa kada gwamnatin jihar ta dauki mataki kan lamarin.”

Ya ce babu wanda zai iya tsige shi domin har yanzu shine Igwe na Nwafia.

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kawo karshen matsalolin tsaron kasar nan, inda yace abubuwa ba za su cigaba da faruwa haka ba a 2021.

Shugaban kasa ya sanar da hakan ne yayin bayyana farin cikinsa a kan sakin daliban GSSS Kankara a jihar Katsina.

Shugaba Buhari ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa ba zai ci amanarsu ba. Ya ce hankalinsa yayi matukar tashi a kan matsalar rashin tsaron da wasu bangarorin kasarnan suke ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel