Buhari ba marowaci bane, ya bani kyautar daloli, in ji Femi Adesina

Buhari ba marowaci bane, ya bani kyautar daloli, in ji Femi Adesina

- Femi Adesina, Kakakin Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba gaskiya bane ikirarin da wasu keyi kan cewa shugaban kasar marowaci ne

- Adesina ya bayyana hakan ne cikin sakon taya Buhari murnar cika shekaru 78 a duniya inda ya bayyana wasu kyautukan kudade da shugaban kasar ya taba masa

- Mista Adesina ya yi kira ga 'yan Najeriya su rika mayarwa shugaban kasar tukwicin karamcinsa sannan ya masa fatan alheri

Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan watsa labarai, Femi Adesina ya karyata ikirarin da wasu ke yi na cewa Shugaba Muhammadu Buhari mutum ne mai rowa.

Kakakin shugaban kasar ya bayyana lokuta biyu da Shugaba Buhari ya masa kyautar kudade na ban mamaki a cikin sakon taya shugaban kasar murnar cika shekaru 78 a duniya.

Buhari ba marowaci bane, ya bani kyautar daloli, in ji Femi Adesina
Buhari ba marowaci bane, ya bani kyautar daloli, in ji Femi Adesina. Hoto: @FemiAdesina
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Hotonun Buratai da maciji a gonarsa ya janyo cece-kuce bayan ya yi muƙus a game da sace daliban Kankara

A cewarsa, a karon farkon za ayi masa nadin sarauta ne a masarautar Mmaku da ke Jihar Enugu kuma kafin tafiyarsa shugaban kasar ya masa babban kyauta domin ya yi jigilar 'yan uwansa da abokan arziki.

A karo na biyun kuma zai tafi kwas ne a kasar China inda nan ma Shugaban kasar ya yi masa ba'a kafin ya masa babban kyautar kudaden kasar waje.

Ya rubuta, "A watan Janairun 2017, za a nada ni sarautar Nwanne di Namba na masarautar Mmaku a JIhar Enugu. Na sanar da shi kafin inyi tafiyar. Wannan mutumin da ke alfaharin 'bai kyauta sosai' ya min kyautan makuden kudade don inyi jigilar yan uwa da abokai zuwa wurin bikin. Nawa ya bani? Ba zan fada ba ballantana ku roke ni.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe yan kasuwa 3 a Zamfara bayan karbar N6m da babura

"A watan Maris din 2018, zan tafi China yin kwas na kwanaki 12 da aka shirya wa manyan jami'an gwamnati daga Afirka. Ya ce in sanar da shi kwana biyu kafin in tafi kuma na tafi ganinsa. In fada maka wani abu Adesina? Na san baka da kudi. Amma kunya ba zai bari ka tambaya ba. 'Mu biyu muka yi dariya, sannan ya bani ambalam dauke da kudaden kasar waje. Nawa ne? Kana tunanin zan fada maka? Inaa!"

Mista Adesina ya kuma ce akawai bukatar 'yan Najeriya su rika mayarwa Buhari tukwuici sannan ya bayyana wasu kyawawan halayen shugaban kasar tare da masa fatan alheri.

A wani labarin, gwamnatin tarayyar Najeriya, a ranar Lahadi ta ce shirin samar da ayyuka na musamman, SPW, guda 774,000 zai fara ne a ranar 5 ga watan Janairun shekarar 2021.

Karamin ministan Kwadago da samar da ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ne ya shaidawa The Nation hakan ranar Lahadi a Abuja.

Shirin samar da ayyukan ga masu sana'o'in hannu na watanni uku inda za a rika biyansu N20,000 duk wata ya samu tsaiko sakamakon rashin jituwa tsakanin ministan da tsohon shugaban hukumar samar da ayyuka ta kasa, NDE, Nasir Ladan da Buhari ya sallama daga aiki makon data gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel