Hotonun Buratai da maciji a gonarsa ya janyo cece-kuce bayan ya yi muƙus a game da sace daliban Kankara

Hotonun Buratai da maciji a gonarsa ya janyo cece-kuce bayan ya yi muƙus a game da sace daliban Kankara

- Hotunan babban hasfin sojojin kasan Najeriya, Tukur Buratai a gonar macizansa ya janyo cece-kuce a dandalin sada zumunta

- Wasu masu tofa albarkacin bakinsu a dandalin sada zumunta suna ganin bai dace irin wannan hotunan su fito ba a yayin da ake kokarin ceto daliban makarantar Kankara

- Kazalika, wasu sun nuna takaicinsu domin killace kansa shugaban sojin ya kamata ya yi ba ziyartar gonarsa ba duba da cewa akwai yiwuwar ya yi mu'amala da wanda ke da korona

Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Lt Janar Tukur Buratai ya ziyarci gonarsa da ke babban titin Keffi zuwa Abuja a Jihar Nasarawa inda ya dauki hotuna da wani damfareren maciji a yayin da ya ke killace kansa bayan wasu sojoji sun kamu da korona.

Direktan wucin gadi, Brig Jana Sagir Musa, ya wallafa hotunan Buratai a ranar Laraba da yamma inda za a iya ganin yana cike da murmushi yayinda ya rike kai da jelar macijin don a dauke shi hotuna, SaharaReporters ta ruwaito.

Hotonun Buratai da maciji a gonarsa ya janyo cece-kuce bayan ya yi muƙus a game da sace daliban Kankara
Hotonun Buratai da maciji a gonarsa ya janyo cece-kuce bayan ya yi muƙus a game da sace daliban Kankara. Hoto: @SaharaReporters
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kama Bishop na coci yana lalata da matar wani faston da ke ƙarƙashinsa

Yanzu ya kai kimanin mako guda bayan da yan bindiga suka afka makarantar sakandare ta maza da ke Kankara suka sace fiye da dalibai 300 kuma Buratai bai yi tsokaci kan lamarin ba duk da kiraye-kirayen da wasu ke yi na neman canja shugabannin tsaron.

A hotunan da aka wallafa a Facebook, Buratai ya ziyarci gonarsa ta macizai, kwanaki kadan bayan an gano wani bidiyo da ke nuna Shugaba Muhammadu Buhari a gonarsa tare da shanu duk da cewa bai ziyarci Kankara don jajantawa iyayen yaran da aka sace ba.

Hotonun Buratai da maciji a gonarsa ya janyo cece-kuce bayan ya yi muƙus a game da sace daliban Kankara
Hotonun Buratai da maciji a gonarsa ya janyo cece-kuce bayan ya yi muƙus a game da sace daliban Kankara. Hoto: @SaharaReporters
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ina fuskantar matsin lamba akan sai na binciki gwamnatocin baya, Gwamnan Bauchi

"Babban hafsan sojojin Najeriya ya ziyarci gonar macizansa a yau," kamar yadda Musa ya rubuta a wani dandalin WhatsApp inda ke nuna hotunan Buratai, duk da cewa kakakin na soji bai yi cikakken bayani kan matakan da sojin ke dauka don ceto yaran ba.

A ranar 13 ga watan Disamba, Janar din soji fiye da 25 sun kamu da Covid 19 bayan halartar taro tare da Janar Olu Irefin wadda cutar da halaka a makon da ta gabata.

Hakan yasa aka dakatar da taron sojojin kuma aka bukaci su killace kansu kamar yadda NCDC ta tanada.

Hotonun Buratai da maciji a gonarsa ya janyo cece-kuce bayan ya yi muƙus a game da sace daliban Kankara
Hotonun Buratai da maciji a gonarsa ya janyo cece-kuce bayan ya yi muƙus a game da sace daliban Kankara. Hoto: SaharaReporters
Asali: Twitter

A wani labarin, gwamnatin tarayyar Najeriya, a ranar Lahadi ta ce shirin samar da ayyuka na musamman, SPW, guda 774,000 zai fara ne a ranar 5 ga watan Janairun shekarar 2021.

Karamin ministan Kwadago da samar da ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ne ya shaidawa The Nation hakan ranar Lahadi a Abuja.

Shirin samar da ayyukan ga masu sana'o'in hannu na watanni uku inda za a rika biyansu N20,000 duk wata ya samu tsaiko sakamakon rashin jituwa tsakanin ministan da tsohon shugaban hukumar samar da ayyuka ta kasa, NDE, Nasir Ladan da Buhari ya sallama daga aiki makon data gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164