FG ta sanar da ranar da ma'aikata 774,000 za su fara aiki

FG ta sanar da ranar da ma'aikata 774,000 za su fara aiki

- Gwamnatin tarayya ta ce a ranar 5 ga watan Janairun 2021 za a fara shirin samar da ayyuka 774,000 ga masu sana'o'in hannu a kasar

- Za a rika biyan masu sana'o'in N20,000 ko wanne wata ne na tsawon watanni uku daga watan Janairu zuwa Maris

- A baya an rika samun matsaloli kan yadda za a aiwatar da shirin hakan ya janyo shugaban kasa ya sallami shugaban NDE, Nasir Ladan

Gwamnatin tarayyar Najeriya, a ranar Lahadi ta ce shirin samar da ayyuka na musamman, SPW, guda 774,000 zai fara ne a ranar 5 ga watan Janairun shekarar 2021.

Karamin ministan Kwadago da samar da ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ne ya shaidawa The Nation hakan ranar Lahadi a Abuja.

FG ta sanar da ranar da ma'aikata 774,000 za su fara aiki
FG ta sanar da ranar da ma'aikata 774,000 za su fara aiki
Source: Twitter

Shirin samar da ayyukan ga masu sana'o'in hannu na watanni uku inda za a rika biyansu N20,000 duk wata ya samu tsaiko sakamakon rashin jituwa tsakanin ministan da tsohon shugaban hukumar samar da ayyuka ta kasa, NDE, Nasir Ladan da Buhari ya sallama daga aiki makon data gabata.

Ministan ya ce an samu 'yan wasu matsaloli ne hakan yasa aka samu dage ranar fara aikin daga lokacin da aka sanar tunda farko.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Wasu da ake zargi da fashi da garkuwa sun tsere daga gidan yari

Tsaikon ba zai rasa nasaba ba harkallon da aka yi tsakanin ministan da tsohon direktan NDE kan wanda ya fi iko kan shirin samar da ayyukan da aiwatar da shi.

An gano cewa korarren shugaban, Ladan ya hada kai tare da majalisar tarayya don dakile Keyamo wanda shine ministan da shirin ke karkashin ma'aikatansa.

Ma'aikatan biyu sun gaza hada kai suyi aiki tare a kan shirin inda Ladan ya rika saba umurnin ministan sannan ya ke hada kai da 'yan majalisar tarayya.

Sau biyu gwamnatin tarayya ta sanar da ranakun fara shirin amma ta dage.

KU KARANTA: Masoyin Buhari ya ce shugaban kasar ya yi murabus bayan sace yan uwansa a Katsina

Duk da fitar da Naira biliyan 26 don samar da kayayyaki kamar yadda Ladan ya fada, har yanzu ba a fara aikin ba.

A ranar Lahadi, Keyamo ya shaidawa wakilin majiyar Legit.ng cewa za a fara aikin a Janairun 2021 sannan za a sanar da fara aikin a hukumance a ranar Laraba bayan taron FEC.

Ministan ya ce yana fatan ba za a samu wata matsala ba yayin aikin tunda an sallami Ladan.

Ya ce, "Mun cimma matsayar fara shirin a ranar 5 ga watan Janairu amma zan sanar a hukumance bayan taron FEC a ranar Laraba. Mun samu wasu matsaloli a Disamba amma mun cimma matsayar fara aikin ranar 5 ga watan Janairu wacce zata fado a ranar Talata.

"Za a fara shirin daga Janairu zuwa Maris na 2021 wadda zai kasance lokacin rani. Don haka, mun shirya. An kawar da duk wani abu da zai bamu matsala."

A wani labarin daban, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a ranar Asabar, ya bukaci gwanatin tarayya da ta sanya dokar ta baci saboda matsalar tsaro a kasar nan bayan da yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai masu yawa a Katsina.

A wata sanarwa Atiku ya bayyana cewa dole gwamnati ta fito da sababbin dabaru ta kuma kyale tsofaffi.

"Sace dalibai masu yawa a makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara a Jihar Katsina, abu ne wanda zai kawo cikas a yakin da ake da rashin tsaro a kasar nan, kuma ina Allah wadai," a cewar Atiku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel