'Yan bindiga sun kashe yan kasuwa 3 a Zamfara bayan karbar N6m da babura

'Yan bindiga sun kashe yan kasuwa 3 a Zamfara bayan karbar N6m da babura

- Mutum uku daga cikin 18 da masu garkuwa da mutane suka sace a Dansadau sun mutu a hannun yan bindigar duk da biyan kudin fansa

- Daya daga cikin wanda abin ya afkawa, Ali Laudi ne ya bayyana cewa mutane uku sun mutu bayan da aka sallame shi, bayan biyan kudin fansa

- Bello Dansadau, shima yana cikin wanda aka yi garkuwa dasu, kuma ya ce ko fitsari zaka to idon ka a rufe yake ga daurin sarka, ya kara da cewa ko makiyin sa ba zai so ya shiga wannan hali ba

'Yan bindiga sun kashe yan kasuwar jihar Zamfara guda uku duk da biyan naira miliyan 6 da sababbin babura a matsayin kudin fansa, kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Yan kasuwar da aka kashe suna cikin yan kasuwar garin dan Sadau 13 da akayi garkuwa dasu sati uku da suka gabata yayin da suke tafe cikin motar bus mai cin mutane 18 a Mashayar Zaki da ke kan titin Gusau - Dan Sadau, kilo mita 82 arewa da Gusau, babban birnin jihar.

Yan bindiga sun kashe yan kasuwa 3 a Zamfara bayan karbar N6m da babura
Yan bindiga sun kashe yan kasuwa 3 a Zamfara bayan karbar N6m da babura. Hoto: @MobiePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan Najeriya basu da shugaba mai tausayinsu, Kungiyar Dattawan Arewa

Daily Trust ta ruwaito cewa masu garkuwar sun tuntubi iyalan wanda suka sace kwana hudu bayan dauke su kuma suka bukaci naira miliyan 80 kafin su sake su.

Wani dan uwan daya daga cikin yan kasuwar, Alhaji Yau Dansadau, ya ce da kyar suka hada miliyan 10 a kudin fansar.

"An samu kusan miliyan 10 kuma duk masu garkuwar sun lashe," a cewar shi. "Bayan an kai musu miliyan 5, sun saki mutum biyu daga cikin su, kuma suka yi alkawarin sakin ragowar washe gari. Wanda aka sako din ko tafiya bai iya yi saboda mugwayen raunika da ke jikin su bayan shafe kwanaki a daure da ankwa," a jawabi da yayi.

KU KARANTA: An kama Bishop na coci yana lalata da matar wani faston da ke ƙarƙashinsa

"Sun dauko su a babura kuma suka kaisu Hannu Tara kilo mita biyu daga inda suka sace su," ya ci gaba da bayani. "Yanzu haka suna nan suna karbar magani. Daya daga cikin su, Ali Laudi, ya shaida mana cewa mutum uku daga cikin su sun mutu a hannun yan bindigar."

Daya daga cikin wanda aka yi garkuwa dasu, Bello Dansadau, ya ce an daure musu ido kuma an daure su da sarka iya tsawon zaman su a hannun yan bindigar kuma basa iya tafiya saboda raunikan kafar su.

"Mun ga bala'i," inji Bello. "Mun sha wahala matuka. Ko bukata ce ta kama mu sai dai mu tafi idon mu a daure. Bazan so irin wannan ya faru ko akan makiyi na ba."

A wani labarin, gwamnatin tarayyar Najeriya, a ranar Lahadi ta ce shirin samar da ayyuka na musamman, SPW, guda 774,000 zai fara ne a ranar 5 ga watan Janairun shekarar 2021.

Karamin ministan Kwadago da samar da ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ne ya shaidawa The Nation hakan ranar Lahadi a Abuja.

Shirin samar da ayyukan ga masu sana'o'in hannu na watanni uku inda za a rika biyansu N20,000 duk wata ya samu tsaiko sakamakon rashin jituwa tsakanin ministan da tsohon shugaban hukumar samar da ayyuka ta kasa, NDE, Nasir Ladan da Buhari ya sallama daga aiki makon data gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel