'An kashe wasu cikinmu': Daya daga cikin daliban Kankara ya bayyana a sabon bidiyo

'An kashe wasu cikinmu': Daya daga cikin daliban Kankara ya bayyana a sabon bidiyo

- A ranar Laraba Masari ya ce Abubakar Shekau makaryaci ne, ba shi ya sace daliban ba

- Martani kan haka, yan ta'addan sun saki sabon bidiyo

Shugaban yan ta'addan Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki bidiyon tabbatarwa gwamnatin tarayya cewa shi da yaransa suka sace daliban makarantar sakandaren kimiya dake Kankara, jihar Katsina ranar Juma'a.

HumAngle ta samu faifain bidiyon wanda ya tabbatar da cewa daliban na hannun Boko Haram.

A bidiyon mai tsawon minti shida da sakwan 30, yaran na kukan neman dauki.

Daya daga cikin daliban wanda yayi magana a Turanci da Hausa ya ce su 520 aka sace amma an kashe wasu saboda gwamnati ta tura jami'an tsaro ceto su.

Ya yi kira ga gwamnatin ta taimaka ta kawo musu dauki, a duba halin da suke ciki.

"Yan kungiyar Abu Shekau sun kama mu; sun kashe wasu cikinmu," dalibin yace.

KU DUBA: Fusatattun matasa sun banka wa barawon waya wuta a Oyo

'An kashe wasu cikinmu': Daya daga cikin daliban Kankara ya bayyana a sabon bidiyo
'An kashe wasu cikinmu': Daya daga cikin daliban Kankara ya bayyana a sabon bidiyo Hoto: @HumAngle
Source: Twitter

Gwamna Bello Masari na jihar Katsina ya ce wadanda suka sace daliban GSSS Kankara, masu garkuwa da mutane ne ba 'yan Boko Haram ba.

Ya musanta maganar Shekau ne a ranar Laraba, inda yace kowa yasan cewa 'yan bindigan gargajiya ne suka sace daliban nan.

Sakamakon haka, yan ta'addan suka sabi bidiyon kuma suka yiwa gwamnan martani.

Ana iya sauraron daya daga cikin yan ta'addan yana yiwa gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, raddi kan karyata Shekau da yayi.

A wani labarin kuwa, shugabannin kungiyar NUT ta malaman Najeriya, sun yi tir a game da dawowar rashin tsaro, inda ake shiga har makarantu ana sace malamai da dalibai.

KU KARANTA: Daga zanga-zanga, mutane masu nakasa sun nakadawa jami'in tsaro duka a kofar majalisa (Bidiyo)

A wani jawabi da Sakatare-Janar na NUT, Mike Ike Ene, ya fitar a makon nan, ya yi kira da babban murya ga gwamnatoci su samar da tsaro a makarantu.

Kamar yadda Daily Trust wanda ta samu wannan jawabi ta bayyana, NUT ta bukaci gwamnatocin tarayya, jihohi da na kananan hukumomi duk su tashi tsaye.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel