Daga zanga-zanga, mutane masu nakasa sun nakadawa jami'in tsaro duka a kofar majalisa (Bidiyo)

Daga zanga-zanga, mutane masu nakasa sun nakadawa jami'in tsaro duka a kofar majalisa (Bidiyo)

- Nakasassu sun fusata ranar Alhamis a majalisar dokokin tarayya dake Abuja

- An samu sabani tsakaninsu da jami'an dake gadi kofar shiga majalisa

Wasu mutane masu nakasa sun garzaya majalisar dokokin tarayya domin zanga-zanga a ranar Alhamis, 17 ga watan Disamba, 2020.

Amma yayin zanga-zangar, wani jami'in tsaro ya gamu da fushinsu inda suka lakada masa mumunan duka.

The Nation ta ruwaito cewa mambobin kungiyar nakasassun yankin Neja Delta, Great-Mind Foundation, sun dira majalisar ne domin ganin sanatocin da ke wakiltansu a majalisar dattawan tarayya.

Sun lashi takobin cewa ba zasu bar majalisa ba har sai sun gana da Sanatocin domin gabatar da bukatunsu.

Daga cikin abubuwan da suke so shine a koya musu ayyukan hannu da kuma murnar ranar makasassu da bikin Kirismeti.

An samu sabani yayinda suke kokarin shiga cikin majalisar.

Nakasassun wanda adadinsu bai gaza 20 ba sun tubure sai sun shiga kuma haka sukayi duk da jami'in tsaron ya hanasu.

An gansu suna suburbudan wani jami'in da yayi kokarin hanasu shiga.

Har da yan sandan dake wajen basu tsira ba, yayinda nakasassun suka yaga musu kaya.

KU KARANTA: Shugaban kasan Faransa, Emmanuel Macron ya kamu da cutar Korona

KU KARANTA: Wani dan majalisar tarayya ya bar PDP, ya koma APC

A bangare guda, shugabannin kungiyar NUT ta malaman Najeriya, sun yi tir a game da dawowar rashin tsaro, inda ake shiga har makarantu ana sace malamai da dalibai.

A wani jawabi da Sakatare-Janar na NUT, Mike Ike Ene, ya fitar a makon nan, ya yi kira da babban murya ga gwamnatoci su samar da tsaro a makarantu.

Dr. Mike Ike Ene ya yi kira ga gwamnati ta samar da tsaro na kullu-yaumin a duka makarantun kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel