NUT ta yi Allah-wadai da satar Dalibai da Malamai, ta bukaci a tsare makarantu
-A ‘yan kwanakin nan ana ta fama da matsalar rashin tsaro a wasu Makarantu
-Kungiyar NUT ta ce idan lamarin ya faskara, to za ta tattara ta shiga yajin-aiki
-NUT ta ce nauyin farko a kan gwamnatoci shi ne tsare rai da dukiyar jama’a
Shugabannin kungiyar NUT ta malaman Najeriya, sun yi tir a game da dawowar rashin tsaro, inda ake shiga har makarantu ana sace malamai da dalibai.
A wani jawabi da Sakatare-Janar na NUT, Mike Ike Ene, ya fitar a makon nan, ya yi kira da babban murya ga gwamnatoci su samar da tsaro a makarantu.
Kamar yadda Daily Trust wanda ta samu wannan jawabi ta bayyana, NUT ta bukaci gwamnatocin tarayya, jihohi da na kananan hukumomi duk su tashi tsaye.
Dr. Mike Ike Ene ya yi kira ga gwamnati ta samar da tsaro na kullu-yaumin a duka makarantun kasar.
KU KARANTA: Yaran Kankara su na dajin Zamfara - Gwamna
Kungiyar NUT ta bakin Sakataren ta na kasa, Dr. Mike Ike Ene, ta yi barazanar cewa malamai za su tafi yajin-aiki idan ba a daina kai hari a makarantu ba.
Dr. Ike Ene ya ce:
“A game da abubuwan da ke faruwa a ‘yan kwanakin nan, za a iya sa kungiyar NUT dole ta rufe wuraren bada karatu idan ‘ya ‘yanta ba su cikin amincin koyar da yara da daura su a kan hanya ba tare da tsoron wasu miyagu, makiya harkar ilmi da cigaban Najeriya su yi awon gaba da su ba..”
Kungiyar malaman ta kuma bayyana cewa idan har ba a kawo karshen ta’adin da ‘yan bindiga su ke yi a makarantu ba, zangon 2019 zai gamu da cikas.
KU KARANTA: Dalibar Makaranta za ta hau kujerar Gwamnan Legas na kwana 1
“A matsayinta na kungiya, NUT ba za ta zura idanu ta na kallo harkar ilmi ya na shan wahala ba.” Ene ya ce babban nauyin gwamnati shi ne bada tsaro.
Bayan kusan mako guda da sace 'yan makarantar GSSS Kankara, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya yi magana,ya bayyana halin da ake ciki.
Gwamna Masari ya bayyana cewa su na tattaunawa da wadanda su ka sace 'daliban Makarantar Kankara ta hannun wasu daga cikin malaman makarantar.
A dadai wannan lokaci kuma mun ji cewa sojoji sun yi alkawarin ceto ‘Yan Makarantan Katsina.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng