Fusatattun matasa sun banka wa barawon waya wuta a Oyo

Fusatattun matasa sun banka wa barawon waya wuta a Oyo

- Wasu samari sun bankawa wani barawon waya wuta a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, bayan shi da abokinsa sun yi yunkurin kwace wayar wani

- Kamar yadda bayanai suka kammala, 'yan fashin wayar, wadanda suke kan babur sun bi motar wani mutum da gudu don kwatar wayarsa amma basu samu nasara ba

- Kafin su kai ga yin kwacen, babur dinsu ya fada rami, hakan yayi sanadiyyar mutuwar daya, mutane kuma suka kona dayan har Lahira

Wasu samari sun banka wa wani, wanda ake zargin dan fashi ne wuta kusa da ofishin jihar da ke Agodi, Ibadan, babban birnin jihar Oyo, jaridar The Punch ta wallafa hakan.

An tattaro bayanai a kan yadda al'amarin ya faru da tsakar rana, yayin da wani Tobi Adebayo, mazaunin Owode, Apata, Ibadan yayi kokarin amsar wayarsa daga hannun wasu da ake zargin 'yan fashi ne, wadanda ba a tabbatar da sunayensu ba.

Sun tafka hatsari a wuraren Agodi da ke garin, yayin kokarin kwatar waya daga hannan mai ita.

Daya daga cikinsu ya mutu take a nan, yayin da wasu samari suka bankawa dayan wuta, duk da ya ji mummunan rauni.

Fusatattun matasa sun banka wa barawon waya wuta a Oyo
Fusatattun matasa sun banka wa barawon waya wuta a Oyo. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

KU KARANTA: Ortom ya bukaci matasan jiharsa da su kare kansu da yankunansu

Wata takarda da jami'in hulda da jama'ar 'yan sandan jihar Oyo, Olugbenga Fadeyi ya fitar, ta bayyana yadda hatsarin ya auku.

A ranar Laraba, 16 ga watan Disamba, da misalin karfe 3:30pm, wasu 'yan fashi a kan babur suka yi wa wani Adebayo Tobi, mai shekaru 27, mazaunin Plot 4, Owode Apata, Ibadan yunkurin fashin wayarsa, kirar Vivo, da kuma wata jakarsa mai dauke da takardu.

"Ganin haka ne yasa suka bi bayan motarsa kirar Toyota Corolla mai lamba, LAGOS KRD 573 CH, kusa da layin Dandaru, wurin da ke kallon ofishin INEC. Sai dai wurin bin shi suka fada wani rami, garin haka babur dinsu ya fadi.

KU KARANTA: Kankara: Masari ya caccaki Shekau, ya ce 'yan makaranta na hannun 'yan bindiga

"Take a nan daya daga cikinsu ya mutu, dayan kuma yaji munanan raunuka. Kafin bayyanar DPO wurin da lamarin ya faru, fiye da mutane 200 sun hada wuta sun banka masa.

"Har yanzu ana cigaba da tattara gawar, kuma ana cigaba da bincike akan al'amarin."

A wani labari na daban, shugaban jam'iyyar APC, kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana shugaba Buhari a matsayin mai kaunar Najeriya, kuma shugaba nagari wanda yake yi wa kasar nan fatan samun cigaba.

A ranar Laraba, 17 ga watan Disamban 2020, ranar da Buhari ya cika shekaru 78, Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su baiwa shugaban hadin kai.

Kamar yadda Tinubu ya ce: "Ni da sauran 'yan kasa nagari, mun taru don mara maka baya don ka samar da cigaba da nasara, wurin cire Najeriya daga kangin da take ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel