Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun saki bidiyon daliban Kankara da suka sace

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun saki bidiyon daliban Kankara da suka sace

- Don karyata jawabin gwamnan Katsina, Boko Haram ta saki bidiyin yaran da ta sace

- A ranar Laraba Masari ya ce Abubakar Shekau makaryaci ne, ba shi ya sace daliban ba

- Daya daga cikin yaran ya yi gajeren jawabi cikin faifan bidiyon

Shugaban yan ta'addan Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki bidiyon tabbatarwa gwamnatin tarayya cewa shi da yaransa suka sace daliban makarantar sakandaren kimiya dake Kankara, jihar Katsina ranar Juma'a.

HumAngle ta samu faifain bidiyon wanda ya tabbatar da cewa daliban na raye kuma yan ta'addan na shirin tattaunawa da gwamnati.

An saki bidiyon mai tsawon minti shida da sakwan 30 inda daya daga cikin yan ta'addan yayi jawabi kuma aka nuna hoton daya daga cikin daliban.

Hakazalika ana iya ganin sauran daliban a bayansa sun yi datti kuma da alamu suna cikin daji.

Daya daga cikin daliban wanda yayi magana a Turanci da Hausa, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tattauna da yan ta'addan kuma ya bada shawaran kada ayi amfani da karfin bindiga.

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun saki bidiyon daliban Kankara da suka sace
Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun saki bidiyon daliban Kankara da suka sace Hoto: @HumAngle
Source: Twitter

A cikin bidiyon ana iya sauraron dalibin yana cewa: "Ku taimaka, wajibi ne ka rusa dukkan yan sa kai, ka kulle dukkan makarantu, amma banda Islamiyya."

"Ku mayar da dukkan Sojojin da kuka turo."

Hakazalika ana iya sauraron daya daga cikin yan ta'addan yana yiwa gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, martani kan karyata Shekau da yayi.

KU KARANTA: Daga zanga-zanga, mutane masu nakasa sun nakadawa jami'in tsaro duka a kofar majalisa (Bidiyo)

Kalli bidiyon:

KARANTA: Wani dan majalisar tarayya ya bar PDP, ya koma APC

Mun kawo muku cewa gwamna Bello Masari na jihar Katsina ya ce wadanda suka sace daliban GSSS Kankara, masu garkuwa da mutane ne ba 'yan Boko Haram ba, Channels Tv ta wallafa.

Ya musanta maganar Shekau ne a ranar Laraba, inda yace kowa yasan cewa 'yan bindigan gargajiya ne suka sace daliban nan.

Satar daliban da har yanzu ba a ga fiye da mutane 333 ba. Sai dai, Masari ya ki amincewa da maganar Shekau.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel