Mun fara magana da 'yan bindiga, an gano inda dalibai suke; Masari ya sanar da Buhari

Mun fara magana da 'yan bindiga, an gano inda dalibai suke; Masari ya sanar da Buhari

- Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ziyarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a Daura

- Bashir Ahmad ya wallafa cewa Masari ya ziyarci Buhari ne domin yi masa jawabi dangane da batun satar dalibai a Kankara

- Masari ya ce 'yan bindigar sun tuntubi gwamnati kuma an fara tattaunawa da su a kan sakin daliban

Gwamnan jihar Katsina, a ranar Litinin, ya sanar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, cewa 'yan bindiga sun tuntubi gwamnatin jiha bayan sun yi awon gaba da daliban makarantar sakandiren Kankara, kamar yadda Channels ta rawaito.

"Gwamnan, wanda ya samu rakiyar mataimakinsa, Manir Yakubu, ya ce 'yan bindigar sun kira kuma tuni an fara tattaunawa dasu a kan kiyaye lafiyarsu da kuma dawo da su gidajensu cikin koshin lafiya," kamar yadda Garba Shehu ya sanar a cikin jawabin da ya fitar.

KARANTA: Sakandire: Dalibai fiye da 500 sun koma makaranta dauke da juna biyu bayan hutun korona

Ya bayyana cewa jami'an tsaro sun hango wurin da daliban suke tare da bayyana cewa ''akwai alamun samun nasara'' dangane da tattaunawar da aka fara.

Mun fara magana da 'yan bindiga, sun tuntubemu; Masari ya sanar da Buhari
Mun fara magana da 'yan bindiga, sun tuntubemu; Masari ya sanar da Buhari @Bashirahmad
Asali: Twitter

A baya Legit.ng ta rawaito cewa A kokarin gwamnati na rubanya kokarinta wajen ceto daliban da aka sace a kamarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara, Masari ya ziyarci Buhari a Daura.

KARANTA: Boko Haram sun kashe wani ango, sun yi amfani da wayarsa wajen sanar cewa "ni dan wuta ne"

A cewar hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, Masari ya ziyarci Buhari ne domin yi masa bayani a kan inda aka kwana dangane da batun daliban makarantar sakandiren Kankara da 'yan bindiga suka kwashe.

Hedikwatar rundunar tsaro (DHQ) ta baza sojojin kasa da na sama domin nemowa da kuma kubutar da daliban makarantar sakandiren kimiyya ta Kankara, jihar Katsina, da 'yan bindiga suka sace, kamar yadda HumAngle ta rawaito.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa CNG sun ce zasu yi tattaki zuwa garin Daura, mahaifar shugaban kasa, Muhamadu Buhari, domin gudanar da zanga-zanga a kan sace dalibai akalla 333 a sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina.

Har yanzu fiye da dalibai 300 ne ake zargin cewa su na hannun 'yan bindigar da suka shiga cikin dakunansu na kwana, a makarantar sakandiren kimiyyya da ke Kankara, su ka yi awon gaba da su.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun dira makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina, da talatainin daren Juma'a zuwa duku-dukun safiyar Asabar, tare da yin awon gaba da dalibai kusan 600.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel