Fiye da ɗaliban sakandire 500 ne ke ɗauke da juna biyu a Benin

Fiye da ɗaliban sakandire 500 ne ke ɗauke da juna biyu a Benin

- Fiye da dalibai mata dari biyar aka samu dauke da juna biyu a makarantun sakandire da ke yankin Borgou

- Kamfanin dillancin labarai na AFB ya rawaito cewa an samu adadin daliban ne daga iya yankin wanda ke gabashin kasar Benin

- Jami'in gwamnati ya alakanta karuwar adadin dalibai masu dauke da juna biyu da dokar kullen da aka saka bayan bullar annobar korona

Kamfanin dillancin labarai na APB ya rawaito cewa daga shekarar 2019 zuwa shekarar 2020, an samu ɗaliban makarantun sakandare sama da 500 ɗauke da juna biyu a yankin Borgou dake arewa maso gabashin ƙasar Benin.

The Nation ta rawaito APB na bayyana cewa, "dalibai mata 547 daga cikin 36,487 da aka yi musu rijista a zangon shekarar 2019 zuwa 2020 suna ɗauke da juna biyu."

Adadin ya haura alkaluman da aka fitar a tsakanin shekarar 2018 zuwa 2019.

KARANTA: Ba mu gamsu ba; magabatan Janar rundunar soji sun bayyana shakku a kan cewa korona ce ajalinsa

Wani jami'in gwamnatin kasar ya alaƙanta ƙaruwar adadin da dokar kulle da aka saka sakamakon ɓullar annobar korona.

Fiye da ɗaliban sakandire 500 ne ke ɗauke da juna biyu a Benin
Fiye da ɗaliban sakandire 500 ne ke ɗauke da juna biyu a Benin
Asali: Getty Images

Duk da cewa babu wata ingantacciyar hujja, masu hasashe na alaƙanta ƙaruwar juna biyun dalibai mata da ɓullar annobar cutar korona.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa hadakar wasu kungiyoyin arewa sun ce zasu yi tattaki zuwa garin Daura, mahaifar shugaban kasa, Muhamadu Buhari, domin gudanar da zanga-zanga akan sace dalibai akalla 333 a sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina.

KARANTA: Boko Haram sun kashe wani ango, sun yi amfani da wayarsa wajen sanar cewa "ni dan wuta ne"

Har yanzu fiye da dalibai 300 ne ake zargin cewa su na hannun 'yan bindigar da suka shiga cikin dakunansu na kwana, a makarantar sakandiren kimiyyya da ke Kankara, su ka yi awon gaba da su, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun dira makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina, da talatainin daren Juma'a zuwa duku-dukun safiyar Asabar, tare da yin awon gaba da dalibai kusan 600.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng