Kungiyar arewa: Za mu yi tattaki har Daura don yi wa Buhari zanga-zanga a kan satar dalibai

Kungiyar arewa: Za mu yi tattaki har Daura don yi wa Buhari zanga-zanga a kan satar dalibai

- Gamayyar kungiyoyin arewacin Nigeria (CNG) ta ce za ta yi tattaki zuwa Daura domin fara zaman dirshan a gaban gidan shugaba Buhari

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ziyarci garin Daura inda zai shafe sati guda

- Wasu 'yan bindiga sun kai hari wata makarantar sakandire da ke Kankara a yayin da Buhari ke jihar Katsina

Hadakar wasu kungiyoyin arewa sun ce zasu yi tattaki zuwa garin Daura, mahaifar shugaban kasa, Muhamadu Buhari, domin gudanar da zanga-zanga a kan sace dalibai akalla 333 a sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina.

Har yanzu fiye da dalibai 300 ne ake zargin cewa su na hannun 'yan bindigar da suka shiga cikin dakunansu na kwana, a makarantar sakandiren kimiyyya da ke Kankara, su ka yi awon gaba da su, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun dira makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina, da talatainin daren Juma'a zuwa duku-dukun safiyar Asabar, tare da yin awon gaba da dalibai kusan 600.

KARANTA: Ya samu nakasa; Mayakin kungiyar Boko Haram ya fallasa halin da Shekau ke ciki

Kakakin gamayyar kungiyoyin, CNG (Bringbackourboys campaign), Abdul-Azeez Suleiman, ya shaidawa Punch cewa zasu yi tattaki tare da yin gangami a Daura daga ranar Litinin har zuwa lokacin da za'a dawo da daliban da aka sace.

Kungiyar arewa: Za mu yi tattaki har Daura don yi wa Buhari zanga-zanga a kan satar dalibai
Kungiyar arewa: Za mu yi tattaki har Daura don yi wa Buhari zanga-zanga a kan satar dalibai @Thecable
Source: Twitter

"Reshen kungiyoyinmu zasu yi dogon tattaki zuwa Daura a jihar Katsina, tunda shugaban kasa yana can, domin neman ya yi wani abu a kan sace daliban.

KARANTA: Ba mu gamsu ba; magabatan Janar a rundunar soji sun bayyana shakku a kan cewa korona ce ajalinsa

"Mambobinmu daga Kano za su fara tattaki daga karamar hukumar Dambatta, inda zasu hadu da mambobinmu daga Jigawa da Katsina a garin Kazaure inda kuma daga nan ne za su hadu da tawagarmu daga Kano a garin Mashi, daga nan kuma mu dunguma zuwa Daura a kafafunmu. Za mu yi birki a gaban gidan shugaba Buhari," a cewarsa.

Kakakin ya bayyana cewar kungiyarsu tana takaicin yadda 'yan bindiga ke cigaba da cin karensu babu babbaka tare da kaddamar da sabbin hare-hare kowacce rana a arewacin Nigeria.

A ranar Lahadi ne Legit.ng ta rawaito cewa mata sun gudanar da zanga zanga a jihar Katsina kan sace yaran makarantar GSSS Kankara.

An gudanar da gangamin ne a yau Lahadi, 13 ga watan Disamba, a harabar makarantar da titunan yankin

Har ila yau gamayyar kungiyoyin arewa sun yi barazanar tara dalibai da matasan domin yin zanga zanga idan har ba'a ceto daliban ba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel