Boko Haram sun kashe wani ango, sun yi amfani da wayarsa wajen sanar cewa "ni dan wuta ne"

Boko Haram sun kashe wani ango, sun yi amfani da wayarsa wajen sanar cewa "ni dan wuta ne"

- Rahotanni sun bayyana yadda mayakan kungiyar Boko Haram suka kashe wani ango sati biyu kacal bayan daurin aurensu

- 'Yan ta'addar sun kama ango Emmanuel Peter, ma'aikacin kungiyar jin kai da ceto, a tsakanin Yobe da Borno

- Bayan sun kashe shi, 'yan ya'addar sun yi amfani da wayarsa ta hannu wajen wallafa sakonni marasa dadi

Emmanuel Peter, wani ma'aikacin jin ƙai da ceto, wanda aka sace a yankin arewa maso gabas, rahotanni sun nuna an kashe shi, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Ƴan tada ƙayar baya sune suka sace shi a garin Jakana kan titin Damaturu, jihar Yobe, zuwa Maiduguri, jihar Borno, a ranar Laraba, amma bayan kwanaki biyu sai ga mamacin ya sanar da rasuwarsa a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook.

Da misalin ƙarfe 12:25am na dare ne hoton Peter na shafin Facebook ya koma baƙi. Haka ma hoto mai biye masa ya canja.

KARANTA: Ba mu gamsu ba; magabatan Janar rundunar soji sun bayyana shakku a kan cewa korona ce ajalinsa

Akwai hotunan kan gilashin waya da ke nuni da chanjawar hotunansa.

Emmanuel Peter shine ya wallafa hakan da kansa a ranar Alhamis, 10 Disamba, 2020 kwana ɗaya bayan an sace shi.

Boko Haram sun kashe wani ango, sun yi amfani da wayarsa wajen sanar cewa "ni dan wuta ne"
Boko Haram sun kashe wani ango, sun yi amfani da wayarsa wajen sanar cewa "ni dan wuta ne" @Thecable
Asali: Twitter

Bayan ƴan mintuna kaɗan, sai gashi an wallafa labarin mutuwarsa a shafinsa.

Sai dai har yanzu an kasa gane waye ya wallafa labarin duk da an fi karfafa tunanin wataƙila ɗaya daga cikin 'yan ta'addar ne.

KARANTA: Bidiyo: An daura auren Suleiman da Ba-Amurkiyya, Jenine, a Kano cikin annashuwa

An wallafa labarin mutuwar tasa kamar haka;

"Sannunku jama'a, na riga na mutu, kar ku damu dani, kawai ku damu da kanku, Baba kayi haƙuri, ba zaka iya samun gawata domin ka yi min suttura ba, sai mun haɗu a ƙiyama. Amma nasan ina wuta, ina fatan za ku zo mu haɗe nan ba da jimawa ba," Kamar yadda aka wallafa.

Ƴan ta'addan sun kashe shi bayan sun gano yana aiki da wata ƙungiyar jin ƙai, duk da ya yi musun cewa bashi da wata alaƙa da ƙungiyar.

'Yan ta'addar sun gano bayanai isassu akansa ta hanyar amfani da wayarsa ta hannu ƙirar iPad.

Makonni biyu kafin rasuwarsa, aka ɗaura auren Peter da matarsa Eyn a wata unguwar talakawa a garin Jimeta,Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Idan har da gaske an kashe shi, to Peter ya bar duniya lokacin da ya kamata ya fara sharɓar romonta.

Arewa maso gabas na fama da matsalar matsanancin rashin tsaro, inda aka sace da yawa tare da kashe wasu, a yayinda kullum gwamnati ke iƙirarin ta na shawo kan lamarim.

A ranar Lahadi ne Legit.ng ta rawaito cewa mata sun gudanar da zanga zanga a jihar Katsina kan sace yaran makarantar GSSS Kankara.

An gudanar da gangamin ne a yau Lahadi, 13 ga watan Disamba, a harabar makarantar da titunan yankin

Har ila yau gamayyar kungiyoyin arewa sun yi barazanar tara dalibai da matasan domin yin zanga zanga idan har ba'a ceto daliban ba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel