- Mutane sun saki jiki da annobar Korona kuma gashi an koma gidan jiya
- Yanzu haka birnin tarayya Abuja da jihar Kaduna ke kan gaba wajen sabbin masu kamuwa
- Hukumar NCDC ta bayyana adadin wadanda suka kamu da cutar ranar Alhamis a fadin tarayya
Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 675 ranar Alhamis a cewar alkaluman hukumar kiyaye yaduwar cututtuka watau NCDC.
Adadin da aka samu ranar Alhamis ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 71,344 a Najeriya.
Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da hakan a daren Alhamis , 11 ga watan Disamba, 2020.
Yayinda adadin masu kamuwa ke raguwa, adadin masu samun waraka daga cutar na kara yawa.
Daga cikin mutane sama da 70,000 da suka kamu, an sallami 65,474 yayinda 1190 suka rigamu gidan gaskiya.
KU KARANTA: FG: Najeriya za ta karba riga-kafin korona miliyan 20

Korona: Mutane 2000 a mako guda, kimanin 700 ranar Alhamis, an koma gidan jiya
Credit: @NCDCgov
Source: Twitter
DUBA NAN: Alkalin Alkalan Kano ya 'yantar da fursunoni 35 a rana guda
Ga jerin adadin wadanda suka kamu a jihohin Najeriya:
FCT-183
Lagos-128
Kaduna-85
Kwara-57
Katsina-50
Plateau-42
Rivers-39
Kano-33
Ondo-21
Ogun-17
Bauchi-10
Sokoto-5
Edo-2
Ekiti-1
Bayelsa-1
Delta-1
Ga jerin jiha-jiha:

Korona: Mutane 2000 a mako guda, kimanin 700 ranar Alhamis, an koma gidan jiya
Credit: @NCDCgov
Source: Twitter
A bangare guda, ministan birnin tarayya Abuja, Muhammadu Musa Bello, ya bayyanawa majalisar dattawan tarayya cewa ya kashe kimanin bilyan 29 domin dakile cutar Korona a Abuja.
Yayin jawabi ga mambobin kwamitin birnin tarayya na majalisar dattawa, Ministan yace an kashe kudaden ne wajen inganta tsaro, kayan abincin rage radadin Korona, da kuma jihohin dake makwabtaka mabukata.
Ya kara da cewa gwamnatin Abuja ta taimakawa mazauna birnin da makwabta da kayayyakin kiwon lafiya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng