FG: Najeriya za ta karba riga-kafin korona miliyan 20
- Sakataren NPHCDA, Faisal Shuaib, ya bayyana matsayarsu a kan batun riga-kafin COVID-19
- A cewarsa, yanzu haka Najeriya tana daya daga cikin kasashe 92 da za su aiwatar da riga-kafin
- Ya ce ana nan ana shirin fara riga kafin a watannin farko na 2021, ga ma'aikatan lafiya da masu karamin karfi
Faisal Shuaib, sakataren NPHCDA, ya yi bayani ak an matsayar da suke a kan COVID-19, a taron PTF da aka yi a Abuja ranar Alhamis.
Ya ce Najeriya tana daya daga cikin kasashen da ke COVAX, karkashin WHO.
Shuaib ya ce kasashe 92 ne suka dunkule wuri guda don duba allurar riga kafin cutar da kuma tabbatar da ingancinta, jaridar The Cable ta wallafa.
KU KARANTA: Boko Haram: Dakarun Najeriya na daya daga cikin zakakuran soji a Afrika, Magashi
A cewarsa, ana sa ran za a samu a kalla riga-kafin mutane miliyan 20, saboda ma'aikatan lafiya da kuma 'yan kasa masu kananan karfi.
"A bisa kokarinmu na tabbatar da ingancin riga-kafin cutar da za a yi a watanni 3 na farkon shekarar 2021. Za mu yi amfani da tsarin Polio wurin gabatar da riga-kafinmu a kan mutane masu kananun karfi," a cewarsa.
"Mun samar da wani kwamitin bayar da shawarwari don tabbatar da an aiwatar da komai yadda ya dace. Sanann za a samar da tsarin raba rigakafin wuri-wuri a fadin Najeriya."
KU KARANTA: Lawan: 'Yan majalisar dattawa ba kansu suke wa aiki ba, Ahmad Lawan
A wani labari na daban, jam'iyyar APC ce take da alhakin tsayar da dan takarar shugabancin kasa na watan Yunin 2023, kamar yadda majiya daga jam'iyyar ta tabbatar wa da Daily Trust a ranar Talata.
Majiyar ta ce idan har a arewa ta fitar da shugaban jam'iyya, kudu za a baiwa damar fitar da dan takarar shugaban kasa, ko kuma arewa ta fitar da dan takarar shugaban kasa, kudu ta fitar da shugaban jam'iyya.
A taron gaggawa da NEC tayi, ta kara wa Mai Mala Buni wa'adin cigaba da shugabancin kwamitin rikon kwaryar na watanni 6. Dama wa'adin shugabancinsa na kwamitin zai kare ne a ranar 25 ga watan Disamba, amma NEC ta kara wa'adin zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2021.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng