Mun kashe N28.5bn kan cutar Korona a Abuja, Ministan FCT Musa Bello

Mun kashe N28.5bn kan cutar Korona a Abuja, Ministan FCT Musa Bello

- Mutane 68 suka kamu da cutar Coronavirus a ranar Talata kadai a birnin tarayya

- Ministan Abuja ya bayyana iri taimakon kayan tallafin da suka yiwa mutanen birnin

- Har yanzu ana samun daruruwan yan Najeriya masu kamuwa da Korona kulli yaumin

Ministan birnin tarayya Abuja, Muhammadu Musa Bello, ya bayyanawa majalisar dattawan tarayya cewa ya kashe kimanin bilyan 29 domin dakile cutar Korona a Abuja.

Yayin jawabi ga mambobin kwamitin birnin tarayya na majalisar dattawa, Ministan yace an kashe kudaden ne wajen inganta tsaro, kayan abincin rage radadin Korona, da kuma jihohin dake makwabtaka mabukata.

Ya kara da cewa gwamnatin Abuja ta taimakawa mazauna birnin da makwabta da kayayyakin kiwon lafiya.

A cewarsa, an yi amfani da yawancin kudin ne wajen samar da kayan abinci ga jama'a, saboda babu wanda ya kawo taimako lokacin da cutar Korona tayi tsauri.

Saboda haka ya bukaci yan majalisan su sake duba kasafin kudin birnin tarayya saboda yawan abubuwan da ke kasa.

Ya ce dubi cikin kasafin kudin da yake bukata wajen yan majalisa shine ta amince da abubuwa masu muhimmanci duk da cutar.

Shugaban kwamitin, Sanata Abubakar Kyari, ya jinjinawa birnin tarayya bisa yadda ta dakile cutar Korona.

KU KARANTA: Buhari ne babban matsalan Najeriya a yau, cewar gamayyar kungiyoyin Arewa

Mun kashe N28.5bn kan cutar Korona a Abuja, Ministan FCT Musa Bello
Mun kashe N28.5bn kan cutar Korona a Abuja, Ministan FCT Musa Bello Hoto: NCDC
Asali: Twitter

KU DUBA: Buhari na fuskantar matsin lamba yayinda dattawan arewa suka tunzura kan kisan Zabarmari

Bangare guda, Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 281 ranar Talata a cewar hukumomin kiwon lafiya.

Adadin da aka samu ranar Talata ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 67,838 a Najeriya.

Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da hakan a daren Talata , 2 ga watan Disamba, 2020.

Yayinda adadin masu kamuwa ke raguwa, adadin masu samun waraka daga cutar na kara yawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel