Alkalin Alkalan Kano ya 'yantar da fursunoni 35 a rana guda

Alkalin Alkalan Kano ya 'yantar da fursunoni 35 a rana guda

- Akalla fursunoni 37 sun samu yanci ranar Alhamis a jihar Kano

- Hakan na cikin yunkurin gwamnatin tarayya na rage cinkoso a gidajen gyara hali

- Kundin tsarin mulki ya baiwa Alkalin Alkalai dama 'yanta fursunoni

Alkalin Alkalan jihar Kano, Nura Sagir Umar, ya 'yantar da fursunoni 37 dake gidajen yarin jihar domin rage cinkoson dake ciki bisa manufar gwamnatin tarayya.

Jawabin da Kakakin hukumar gyara halin jihar, DSC Musbahu Lawal, ya ce an tsawatar da wadanda aka saki kuma an shawarcesu su kasance mutanen kirki kuma suyi amfani da daman wajen yiwa kawunansu abubuwan arziki.

Bayan haka an baiwa kowanne cikin N2,000 matsayin kudin mota domin su koma wajen iyalansu, Daily Trust ta ruwaito.

A bangarensa, kwantrolan hukumar gidajen gyara hali na jihar, Suleiman Suleiman, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Yunusa Lawan, ya yi kira ga fursunonin su nisanci abubuwa laifi kuma su kasance masu bin doka.

DUBA NAN: Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka Soji 10, sun kwace sabon motar yaki

Alkalin Alkalan Kano ya 'yantar da fursunoni 35 a rana guda
Alkalin Alkalan Kano ya 'yantar da fursunoni 35 a rana guda
Source: UGC

KU KARANTA: Gaskiya mun gaji: Sojojin dake yaki da Boko Haram tun 2016 a Borno sun koka

A bangare guda, wasu yan baranda a ranar Alhamis sun kai hari majalisar dokokin jihar Ogun kuma sun yi awon gaba da sandar iko na majalisar.

Channels TV ta ce Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da labarin.

Ya ce matasan sun fasa cikin majalisan ne da safiyar Alhamis kuma suka dauke sandar.

Ya ce amma an samu kwato kan sanda dake dauke da tambarin Najeriya, har yanzu ana neman sauran jikin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel