Mu'azu Gusau: An nada sabon shugaba a jami'ar tarayya ta Gusau

Mu'azu Gusau: An nada sabon shugaba a jami'ar tarayya ta Gusau

- Farfesa Muazu Gusau ya zama sabon shugaban jami'ar gwamnatin tarayya da ke Gusau, jihar Zamfara

- Mutane guda 25 ne suka gabatar da sunayensu don neman kujerar shugabancin jami'ar amma Mu'azu Gusau ne ya yi nasara

- Muazu Gusau ya karbi ragamar shugabancin jami'ar ne daga hannun Farfesa Magaji Garba wadda ya shafe shekaru 10 yana shugabanci

An nada Farfesa Muazu Gusau a matsayin sabon shugaban jami'ar gwamnatin tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara, Daily Nigerian ta ruwaito.

Sanarwar da jami'in watsa labarai na jami'ar, Umar Usman ya fitar ta ce, mutane 25 suka nemi cike gurbin bayan da aka tallata amma Farfesa Mu'azu Gusau ne ya yi nasarar doke su.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe Kanawa 16 a titin Kaduna zuwa Abuja

Farfesa Mu'azu, wadda shine shugaban jami'an na uku, zai yi aiki na wa'adin shekaru biyar a karo na farko wadda zata fara daga ranar 10 ga watan Fabarairun shekarar 2021.

Sabon shugaban wanda kwararre na a fannin nazarin guba wato toxicology ya yi digirinsa na uku ne a jami'ar Surrey da ke Birtaniya.

Zai karbi ragamar shugabancin jami'ar daga hannun Farfesa Magaji Garba wanda shi kuma zai koma jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda dama a can ya ke koyarwa.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun ce sun kashe kasurgumin dan bindiga a Niger

Farfesa Magaji ya shugabanci jami'ar na tsawon shekaru biyu wato wa'adi biyu kenan.

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel