'Yan bindiga sun kashe Kanawa 16 a titin Kaduna zuwa Abuja

'Yan bindiga sun kashe Kanawa 16 a titin Kaduna zuwa Abuja

- Yan bindiga sun yi sanadiyar mutuwar mutane 16 yan asalin jihar Kano a kan hanyar su ta dawowa kano daga Abuja a babban titin Kaduna zuwa Abuja

- Wata majiya daga karamar hukumar Danbatta ta tabbatar da cewa mutanen yan asalin karamar hukumar sun gamu da ajalinsu bayan da yan bindiga suka harbi tayar bus din da suke ciki

- Gwamnatin jihar ta jajantawa iyalan mamatan tare da bayyana bakin ciki da bacin rai tare da jajantawa yan karamar hukumar Danbatta

Mutanen da basu gaza mutane 16 yan asalin karamar hukumar Danbatta ne suka gamu da ajalinsu a babban titin Kaduna zuwa Abuja, Vanguard ta ruwaito.

Wata majiya daga karamar hukumar Danbatta, wanda yayi bayani cikin bacin rai, ya ce wanda suka rasa ran nasu duk maza ne, sun rasu ranar Talata lokacin da yan bindiga su ka harbi tayar motar su lokacin da take dauko su daga Abuja don dawowa Kano.

Yan bindiga sun kashe yan asalin jihar Kano 16 titin Kaduna zuwa Abuja
Yan bindiga sun kashe yan asalin jihar Kano 16 titin Kaduna zuwa Abuja. Hoto: @Vanguardngrnews
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya ƙara matasan da za a ɗiba a N-Power zuwa miliyan ɗaya

Majiyar ta shaida cewa lamarin ne yayi sanadiyar hadarin da ya janyo mutuwar mutanen.

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, a ranar Alhamis, ya tabbatar da kisan mutanen kuma ya mika ta'aziyyar sa ga Iyalan mamatan ta bakin Sakataren yada labaran sa Abba Anwar.

Gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki da bacin rai.

Sanarwar ta ce: "mun kaɗu kwarai da mummunan labarin rasuwar mutane 16 yan asalin karamar hukumar Danbatta a kan babban titin Kaduna zuwa Abuja, wanda su ke dawowa daga Abuja zuwa Kano, sanadiyar hari daga yan bindigar da ba a san ko su waye ba."

Labarin abin bakin ciki ne da bacin rai.

KU KARANTA: Mafi yawancin 'yan matan da ake latsa wa a manyan makarantu daƙiƙai ne, in ji Gwamna Ayade

"Allah ya karbi shahadarsu ya kuma hukunta wanda suka aikata musu wannan ta'addanci. Ba abin da ya fi wannan wannan bakin ciki," a cewar gwamnan.

Ya bukaci mutane su saka mamatan cikin addu'a ya kuma roki "Allah ya baiwa iyalan su hakurin jure rashin su."

"A madadin gwamnati da al'ummar jihar Kano. Ina mika sakon ta'aziyya ga Iyalan wanda suka rasu da al'ummar Danbatta game da wannan iffila'i.

"Allah ya gafarta musu ya kuma yafe kurakuren su ya basu ladan ayyukan alherin su," inji Ganduje.

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel