Kaduna: El-Rufa'i zai sake saka dokar kulle sakamakon hauhawar alkaluman korona

Kaduna: El-Rufa'i zai sake saka dokar kulle sakamakon hauhawar alkaluman korona

- 'Yan Najeriya sun fara nuna damuwarsu dangane da hauhawar alkaluman masu kamuwa da cutar korona da ake samu

- Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya yi kurarin cewa zai sake saka dokar kulle a fadin jiharsa

- A cewar gwamnan, zai sake saka dokar ne idan jama'a basu kiyaye ba ko kuma idan alkaluman masu kamuwa da cutar suka cigaba da hauhawa

Mallam Nasir El-Rufa'i, gwamnan jihar Kaduna, ya ce akwai yiwuwar zai sake saka dokar kulle saboda hauhawar alkaluman masu kamuwa da cutar korona da ake samu a jihar da fadin kasa.

Abdallah Yunus Abdallah, mai taimakawa El-Rufa'i a bangaren watsa labarai, ya ce gwamnati za ta dauki wannan mataki ne saboda kare hakkin kare rayukan mutanen jihar ya rataya ne a wuyan gwamnan.

A cewarsa, gwamnan ya yi wannan jan kunnen ne saboda alhakinsa ne ya kula da lafiyar mutanen jihar Kaduna, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

KARANTA: PANDEF: Muna son jin amsar tambayoyinmu guda uku daga bakin Buhari

Kaduna: El-Rufa'i zai sake saka dokar kulle sakamakon hauhawar alkaluman korona
Kaduna: El-Rufa'i zai sake saka dokar kulle sakamakon hauhawar alkaluman korona @Daily_trust
Asali: Twitter

Hadimin gwamnan ya kara da cewa babu abinda zai hana gwamnan Kaduna ya sake saka dokar kullen jama'a matukar basu kiyaye sharudan kare kai domin dakile yaduwar cutar ba ko kuma idan alkaluman masu kamuwa da cutar suka cigaba da hauhawa.

KARANTA: Gayyatar Buhari: Majalisar dattijai ta juyawa majalisar wakilai baya

"Yaki da cutar korona aiki ne da ya rataya a wuyan dukan jama'a, ba iya gwamnati kadai ba, a saboda haka ya zama wajibi a kan mutane su kula tare da yin biyayya ga dokoki da matakan kare kai domin dakile yaduwar cutar, a cewarsa.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 550 ranar Talata a cewar alkaluman hukumar NCDC.

Adadin da aka samu ranar Talata ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 70,195 a Najeriya, kamar yadda hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta sanar a daren Talata, 8 ga watan Disamba, 2020.

Yayinda adadin masu kamuwa ke raguwa, adadin masu samun waraka daga cutar na kara yawa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel