Gayyatar Buhari: Majalisar dattijai ta juyawa majalisar wakilai baya
- Shugaba Buhari, a satin da ya gabata, ya amsa cewa zai bayyana a gaban zaman majalisa na hadin gwuiwa, kamar yadda rahotanni suka wallaf
- Daga baya an sanar da cewa Buhari zai bayyana a gaban majalisa a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba
- Ana tsaka da tababa a kan bayyanar shugaba Buhari, sai ga shi majalisar dattijai ta nesanta kanta da batun
Sanatoci a ranar Laraba sun nisanta kansu daga gayyatar da ƴan majalisar wakilai suka yi wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, don ya zo ya yi bayani kan ta'azzarar rashin tsaro a faɗin ƙasar nan, kamar yadda The Nation ta rawaito.
Wannan ya zo ne lokacin da mataimakin shugaban sanatoci, Ovie Omo-Agege, ya ce hakan ya saɓawa kundin doka sannan kuma ya sauka daga turba da tsarin kowacce irin majalisa ta gayyaci shugaban ƙasa ya gurfana a gabanta.
Shi ma Shugaban kwamitin Sanatoci kan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Sanata Ajibola Basiru (Osun ta tsakiya) ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa Sanatoci ba su da alaƙa ko kaɗan da gayyatar shugaban ƙasar da majalisar wakilai ta yi.
KARANTA: Zanga-zanga: Buhari ya koka da kafafen yada labarai na ketare, ya ambaci sunan guda biyu
Ya ce tunda Sanatoci basu gayyaci Shugaban ƙasar ba, ba su so a jefasu cikin sarƙaƙiyar ko shugaban ƙasar zai amsa gayyatar ko akasin haka.
Basiru ya ce; "ba nine mai magana da yawun Sanatocin Najeriya ba. Amma babu sa hannun sanatoci kan gayyatar shugaban ƙasa ya zo ya yi bayani akan sha'anin tsaron ƙasa.
"Ina tsammanin dukkan wata buƙatar gayyata ko kiran shugaban ƙasa za'a tura ta zuwa majalisar wakilai.
"Majalisun mu sun sha ban ban da juna. Wannan ne yasa tsarinmu da dokokin mu suka bambanta, hakan ne yasa ake buƙatar haɗin kai a tsakaninmu don zartar da doka ko kuɗiri."
"Akan wannan batun, babu wani batun haɗaka tsakanin mu. Abin da ake da shi shine haɗin kan majalisar wakilai kaɗai."
DUBA WANNAN: FG: Mutum 38,051 'yan kasashen ketare sun nuna sha'awar zama 'yan Nigeria a cikin shekara biyu
"Kuma na yarda majalisar wakilai zata iya faɗa muku dalilin da yasa aka miƙa gayyatar da kuma abin da zai faru akai"
"A iya sanin Sanatoci, ba mu gayyaci shugaban ƙasa ba, kuma ba ma son mu saka kanmu cikin wannan sarƙakiyar akan ko shugaban ƙasa zai halarta ko akasin haka."
"A iya sanina, ban da wata masaniyar haɗaka tsakanin mu da majalisar zartarwa gobe."
Dangane da maganar Abubakar Malami,Alƙalin alƙalai kuma ministan shari'a, da ya ce majalisar zartarwa bata da ikon gayyatar shugaban ƙasa ya ce.;
"Ni masanin doka ne, ban karanta abin da Malami yace ba, idan na karanta, kuma naga ya shafi sanatocin Najeriya zan maida martani.Ba zan iya maida martani kan raɗe raɗi ba.
A baya Legit.ng ta rawaito cewa gwamnatin tarayya ta sanar da cewa fiye da mutum dubu talatin da takwas daga kasashen ketare sun nuna sha'awar son zama 'yan Nigeria.
Dakta Shuaib Begore, babban sakatare a ma'aikatar harkokin cikin gida, ya sanar da hakan a Abuja yayin wani taro.
Matasa daga Nigeria kan saka rayuwarsu cikin hatsari domin samun damar tsallakawa zuwa kasashen duniya musamman turai
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng