An koma gidan jiya, sabbin mutane 550 sun kamu da cutar Korona a Najeriya
- Mutane sun fara sakin jiki kan lamarin annobar Korona kuma daruruwan yan Najeriya na sake kamuwa
- Gwamnatin tarayya ta shawarci masu shirye-shiryen bikin Kirismeti su bi hankali
- Hukumar NCDC ta bayyana adadin wadanda suka kamu da cutar ranar Talata a fadin tarayya
Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 550 ranar Talata a cewar alkaluman hukumar kiwon lafiya, NCDC.
Adadin da aka samu ranar Talata ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 70,195 a Najeriya.
Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da hakan a daren Talata , 8 ga watan Disamba, 2020.
Yayinda adadin masu kamuwa ke raguwa, adadin masu samun waraka daga cutar na kara yawa.
Daga cikin mutane sama da 70,000 da suka kamu, an sallami 65,110 yayinda 1182 suka rigamu gidan gaskiya.
Ga jerin adadin wadanda suka kamu a jihohin Najeriya:
Lagos-219
FCT-168
Kaduna-52
Kwara-19
Kano-15
Rivers-15
Sokoto-10
Enugu-9
Gombe-8
Plateau-7
Osun-7
Anambra-5
Oyo-5
Jigawa-4
Ogun-4
Bauchi-2
Edo-1
KU KARANTA: Dan majalisa, Hernan Hembe, ya sauya sheka jam'iyyar APC
Ga jerin jiha-jiha:
KU KARANTA: Zan bude boda nan ba da dadewa ba, Buhari
A bangare guda, ministan birnin tarayya Abuja, Muhammadu Musa Bello, ya bayyanawa majalisar dattawan tarayya cewa ya kashe kimanin bilyan 29 domin dakile cutar Korona a Abuja.
Yayin jawabi ga mambobin kwamitin birnin tarayya na majalisar dattawa, Ministan yace an kashe kudaden ne wajen inganta tsaro, kayan abincin rage radadin Korona, da kuma jihohin dake makwabtaka mabukata.
Ya kara da cewa gwamnatin Abuja ta taimakawa mazauna birnin da makwabta da kayayyakin kiwon lafiya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng