Ya kamata Buhari ya bayyana dalilin da yasa bai sauke shugabannin tsaro ba

Ya kamata Buhari ya bayyana dalilin da yasa bai sauke shugabannin tsaro ba

- Har yanzu 'yan Nigeria na cigaba da yin korafi a kan cigaba da aiki da shugaba Buhari ke yi da shugabannin hukumomin tsaro

- Shugaba Buhari ya yi burus da dukkan kiraye kirayen neman ya sauke shugabannin hukumomin tsaro

Ƙungiyar cigaban yankin Niger Delta (PANDEF) ta yi kira ga ƴan majalisar tarayya da suyi amfani da wannan damar da ake tsammanin ziyarar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari domin su tambaye shi don jin ba'asin dalilin da ya hana shi tsige shugabannin tsaro a halin taɓarɓarewa da ta'azar rashi tsaro a ƙasa.

Mai magana da yawun ƙungiyar PANDEF, Mr. Ken Robinson, shine wanda ya yi kiran ya yin wata hira da jaridar The Punch a ranar Talata.

Ya ce; "Kamata ya yi ayi watsi da lamarin siyasa don cimma buƙatar tattaunawar, wanda shine inganta tsaro."

"Maƙasudin wannan taro shine tattaunawa akan matsalar rashin tsaro, wannan shine babban ƙalubale, kuma ya shafi al'amuran tattalin arziƙin ƙasa."

KARANTA: Gayyatar Buhari: Majalisar dattijai ta juyawa majalisar wakilai baya

Buhari ya bayyana dalilin da yasa bai sauke shugabannin tsaro ba
Buhari ya bayyana dalilin da yasa bai sauke shugabannin tsaro ba @Thecable
Source: Twitter

"Ƴan Najeriya sun shiga firgici gami da halin ɗar-ɗar saboda suna tunanin rayukansu ba su tsira ba. A halin da ake ciki Najeriya ita ce ƙasa ta uku mafi ta'azzara a ta'addanci a duniya."

"To, muna tsammanin ƴan majalisa zasu tsaya tsayin daka su sami ƙwarin guiwar tambayar shugaban ƙasa musamman akan dalilin da yasa bai tsige shugabannin tsaro ba duk da gazawarsu wajen taɓuka wata rawar azo a gani da kuma taɓarɓarewar sha'anin tsaro."

KARANTA: FG: Mutum 38,051 'yan kasashen ketare sun nuna sha'awar zama 'yan Nigeria a cikin shekara biyu

"Yan majalisu su fito ɓaro-ɓaro ba tare da shakkar kowa ba, su tambaye shi game da shirinsa wajen yaƙar kashe kashe, satar mutane, fashi da makami kuma su tabbatar an daƙile matsalar rashin tsaro ba tare da ɓata lokaci ba."

"A tambayi shugaban ƙasa matakan da yake ɗauka wajen gyara da sauya fasalin Najeriya. A kau da batun siyasa ko jam'iyya wajen tambayar Shugaba Buhari."

"Su tambaye shi akan naɗe naɗen gwamnati masu ɗauke da naƙasu a cikinsu, duk da dai ba shine ainihin dalilin ziyartar tasa ba"

"Idan aka cigaba,a saka shi ya tsige shugabannin tsaro,idan da hali ma a bashi wa'adin tsige su take a cikin ginin majalisar."

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya koka da halayyar wasu kafafen yada labarai na kasashen ketare.

Buhari ya zargi kafafen yada labaran ketare, musamman BBC da CNN, da jirgewa bangare guda a rahotannin da suka yada dangane da zanga-zangar EndSARS

Gidan talabijin na CNN ya wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna cewa dakarun soji sun budewa fararen hula a Lekki, Legas.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel