Matata ta tare da wani namiji a barikin mu, sojan mai ritaya ya shaidawa kotu

Matata ta tare da wani namiji a barikin mu, sojan mai ritaya ya shaidawa kotu

- Wani sojan sama mai murabus ya roki wata kotu da ta raba auren shi da matarsa da yace ta hana shi ganin yayansa

- Ya kuma shaidawa kotu cewa matar ta tare da wani namijin daban bayan da shi ya tafi Borno aiki tare da kai karamin dansu wajen mahaifiyarta ba tare da izininsa ba

- Matar ta musanta zargin, kuma ta ce shi ne baya turo musu kudin abinci shiyasa ta kaisu kauye ta kuma tare a gidan kawar ta saboda albashinta ba zai isa ita da yara ba

Wani sojan sama mai ritaya dan shekara 39, Richard Imana ya roki wata kotun gargajiya a Iyana-Ipaja da ke jihar Lagos da ta raba aurensa, saboda wulakanta shi da hana shi ganin yayansa da matar sa ke yi.

Richard ya shaidawa kotu cewa matarsa, Nkem, ta bar gidan auren ta, ta kuma bi wani mutumin a barikin da ya ke zaune da iyalansa. Ya ce matar ta koma wajen mutumin lokacin da shi ya ke aiki a Borno, Vanguard ta ruwaito.

Matata tare da wani namiji a bariki, sojan mai ritaya ya shaidawa kotu
Matata tare da wani namiji a bariki, sojan mai ritaya ya shaidawa kotu. Hoto daga @thecableng
Source: UGC

DUBA WANNAN: Mafi yawancin 'yan matan da ake latsa wa a manyan makarantu daƙiƙai ne, in ji Gwamna Ayade

"Matata ta rufe bangare na, ta tare a gidan wani lokacin ina Borno. Ta guje ni saboda wani, nayi murabus don kula da yayanmu.

"Akwai lokacin da bani da lafiya likita ya bukaci ta sanya hannu a takardu don ayi min magani amma ta ƙi.

" Ta hana ni ganin yara na, ta dauke karamin ta kaiwa mahaifiyar ta ba tare da izini na ba," a cewar mai karar.

Da take maida martani, Nkem mai shekara 34 ta ce ita fa ba wajen wanda ta koma, ta je wajen kawarta ne wadda ta ke makwabciyar ta saboda mijin ta ya daina tura mata kudin abinci.

KU KARANTA: Yan sanda sun ce sun kashe kasurgumin dan bindiga a Niger

"Na kai yaya na kauye lokacin da hakan ke faruwa saboda mahaifinsu baya turo kudin abincin su.

"Na kwashe kaya na cikin fushi, saboda lokacin, albashi na N25, 000 kuma bazai isa ni da yara ba," a nata jawabin.

Ta ce ya shigar da karar ne a bisa rashin fahimta.

Sai dai duk ma'auratan biyu sun bayyana cewa har yanzu su na kaunar junansu sai dai kawai rashin samun lokacin tattaunawa.

Alkalin kotun, Prince Adewale Adegoke ya gargadi Nkem kan tarewa tare da kawar ta.

Ya kuma umarci a dawo da karamin dan su Lagos a kuma hada shi da baban shi.

Adegoke ya ce su zauna lafiya ya kuma dage cigaba da sauraron ƙarar zuwa 15 ga Disamba don daukar mataki.

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.

Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel