Mafi yawancin 'yan matan da ake latsa wa a manyan makarantu daƙiƙai ne, in ji Gwamna Ayade

Mafi yawancin 'yan matan da ake latsa wa a manyan makarantu daƙiƙai ne, in ji Gwamna Ayade

- Gwamnan Cross Rivers Ben Ayade ya ce mafi yawancin matan da ake latsa wa a jami'o'i daƙiƙai ne

- Ben Ayade ya bayyana hakan ne yayin wani tattaki da aka yi a Calabar na yaki da cin zarafin mutane saboda jinsi

- Ayade ya ce mafi yawancin matan da ke irin wannan korafin sukan tafi wurin malamai ne neman maki a sirrince

Gwamnan Jihar Cross Rivers Farfesa Ben Ayade ya ce galibin matan jami'a da ake latsa wa daƙiƙai ne kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaki ta kilomita daya da ake yi a Calabar saboda yaki da cin zarafin mutane saboda jinsi a jihar.

Mafi yawancin 'yan matan da malamai ke haike wa dakikai ne, Gwamna Ayade
Mafi yawancin 'yan matan da malamai ke haike wa dakikai ne, Gwamna Ayade. Hoto: @TheNationNews
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Dakatar da ni da jam'iyya ta yi ya saba doka, tsohon mataimakin shugaban APC, Eta

Ayade ya samu wakilcin Ms Tina Agbor, sakataren gwamnatin jihar a wurin taron da ake yi wa lakabi da “Orange the World: Leave No One Behind, End Violence against Women and Girls.”

Da ya ke bawa yan matan shawara, ya ce, "Saboda al'umma suna sa ran ki zama cikakken mace kuma kiyi aure, mata da dama suna zaune da mazaje da ke galaza musu".

"A matsayin ki na mace, ya kamata ki daraja kanki domin maza su rika ganin mutuncin ki domin idan kika zubar da mutuncin ki, maza za su dinga neman wasa da hankalinki.

KU KARANTA: Majalisa bata da ikon tilasta wa Buhari ya bayyana gabanta, in ji Malami

"A matsayinki na daliba a jami'a, ki dage wurin karatunki domin babu wanda zai nemi ya raina miki wayyo idan ya san kin san abinda kike yi.

"Wasu daga cikin daliban jami'a da ke cewa ana latsa su dakikai ne da ke zuwa wurin malamai a sirrince domin rokon maki."

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.

Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel