Da duminsa: Buhari ya amince bayyana gaban 'yan majalisa a kan rashin tsaro, Gbajabiamila

Da duminsa: Buhari ya amince bayyana gaban 'yan majalisa a kan rashin tsaro, Gbajabiamila

- Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da zama da 'yan majalisar wakilai nan kusa

- Hakan ya biyo bayan yadda 'yan majalisar suka rude, suka kidime kuma suka gigice

- Majalisar ta dauki zafi a ranar Talata bayan an kawo batun kashe-kashen manoma 43 na jihar Borno

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da zama da 'yan majalisar wakilai don tattaunawa a kan matsalar rashin tsaro, kamar yadda 'yan majalisar suka bukata.

Kamar yadda kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila yace, an tsayar da ranar da za a tattauna, kuma nan kusa za a sanar da lokacin.

Ya fadi hakan a ranar Laraba, inda yace Shugaban kasa ya fi kowa shiga cikin damuwa a kan yanayin rashin tsaron da kasarsa take ciki, kuma zai yi wa 'yan Najeriya magana ta wurin wakilansu nan kusa.

Da duminsa: Buhari ya amince da yi wa 'yan majalisar wakilai jawabi, Gbajabiamila
Da duminsa: Buhari ya amince da yi wa 'yan majalisar wakilai jawabi, Gbajabiamila. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: UGC

KU KARANTA: Kisan manoma 73 a Zabarmari: Sheikh Ahmad Gumi ya aike wa Buhari muhimmin sako

Shugaban kasa ya yanke wannan shawarar ne a ranar Talata lokacin da majalisar ta dauki zafi a kan kashe-kashen manoman shinkafa 43 na jihar Borno, wanda 'yan Boko Haram suka aiwatar.

Bayan kawo maganar majalisa, duk 'yan majalisar suka kidime kuma sun rude, kowa yana tofa albarkacin bakinsa.

Ganin hakan ne kakakin majalisar yace ba zai kyautu a yanke wani hukunci a kan harkar tsaro ba, ba tare da tuntubar shugaban kasa ba.

Kakakin ya kwatanta wannan taro da za a yi a matsayin cigaba, wanda kowa yake sa ran ganin nasara, Channels TV ta wallafa.

KU KARANTA: Da duminsa: PDP ta janye daga zabukan kananan hukumomi a Kano, ta fadi dalili

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana damuwarsa a kan rashin damar bayar da umarni ga 'yan sanda a kan kashe-kashe da tabarbarewar tsaro a Najeriya.

A wata tattaunawa da gidan talabijin din Channels suka yi da gwamnan a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba, El-Rufai ya bayyana damuwar da shi da takwarorinsa na sauran jihohi suka shiga a kan harkokin tsaron kasar nan.

Gwamnan ya ce ana kiran gwamnoni da shugabannin jami'an tsaro ne a baki kawai, amma a zahiri, basu da damar tankwara 'yan sanda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel