Kisan manoma 73 a Zabarmari: Sheikh Ahmad Gumi ya aike wa Buhari muhimmin sako
- Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi ya bukaci Buhari yayi murabus
- Ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya gaza a mulkinsa, ya kasa kare lafiyar al'ummar Najeriya
- Ya ce kullum 'yan Najeriya cike suke da fargaba da tashin hankali saboda kashe-kashen 'yan ta'adda
Sanannen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda babban malamin ya bukaci yayi murabus sakamakon tabarbarewar harkar tsaro a Najeriya.
Hakan ya biyo bayan yankan ragon da 'yan Boko Haram suka yi wa manoma 43 a kauyen Zabarmari da ke jihar Borno.
Bayan faruwar lamarin, kasashen ketare da dama sun nuna alhininsu a kai, sannan manyan malaman addini sun fito fili sun nuna takaicinsu a kan aukuwar lamarin, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: Da duminsa: ISWAP sun yi awon gaba da jami'an gwamnatin Borno 3 a Damasak
Sheikh Gumi ya nuna matukar takaicinsa a kan faruwar lamarin kuma a karkashin mulki shugaban kasa Buhari, ya ce al'amarin ya tsananta fiye da na mulkin da ya gabata.
Ya ce babu wani uzuri da ya kamata a bai wa gwamnatin Buhari don ga dukkan alamu ta gaza wurin bayar da kariya ga al'ummar Najeriya.
KU KARANTA: 'Yan sandan da ya dace su yaki 'yan bindiga ne ke rike jakar matan manya, El-Rufai
Sheikh Gumi ya koka a kan yadda kullum ake asarar rayuka sakamakon gazawar gwamnati, musamman yadda al'amarin yake shafar wadanda ba su ji ba ba su gani ba.
A wani labari na daban, a ranar Litinin, rundunar sojin Najeriya ta nuna takaicin yadda wasu 'yan arewa maso gabas suke kin bai wa jami'an tsaro bayanai wadanda za su taimaka wurin bincike.
A kalla manoma 43 ake zargin 'yan Boko Haram sun kashe a Zabarmari, jihar Borno a ranar Asabar, Channels TV ta ruwaito.
UN ta ce kisan da aka yi ya kai mutane 110. Sannan wannan harin da aka kai na kwanan nan ya yi tsanani a cikin hare-haren arewa maso gabas da ake kaiwa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng