Da duminsa: PDP ta janye daga zabukan kananan hukumomi a Kano, ta fadi dalili

Da duminsa: PDP ta janye daga zabukan kananan hukumomi a Kano, ta fadi dalili

- Jam'iyyar PDP reshen jihar Kano ta sanar da janyewa daga zabukan kananan hukumomi na jihar

- Ta sanar da hakan ne a ranar Juma'a ga manema labarai ta hannun shugaban kwamitin rikon kwaryarta a jihar

- Ta ce tana da tabbacin ba za a yi zaben tsakani da Allah ba kuma salo ne na kwashe kudaden jihar da APC ta fito da shi

Babbar jam'iyyar adawa a jihar Kano, PDP, karkashin bangarenta na Kwankwasiyya ta ce ta janye daga zabukan kananan hukumomi da za a gudanar a ranar 16 ga watan Janairu mai zuwa, Daily Trust ta wallafa.

Wannan hukuncin an sanar da shi ne a ranar Talata a yayin taron manema labarai wanda kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar a jihar, wanda Dr. Danladi Albdulhameed tare da dan takarar kujerar gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, tare da sauran 'yan Kwankwasiyya suka shirya.

KU KARANTA: Rade-radin sabuwar zanga-zanga: FG ta sanar da tsatsauran matakin da za ta dauka

Da duminsa: PDP ta janye daga zabukan kananan hukumomi a Kano, ta fadi dalili
Da duminsa: PDP ta janye daga zabukan kananan hukumomi a Kano, ta fadi dalili. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan sandan da ya dace su yaki 'yan bindiga ne ke rike jakar matan manya, El-Rufai

Abdulhameed ya sanar da cewa jam'iyyar ta sakankance cewa "Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Ganduje ba za ta iya yin zaben gaskiya."

Hakan yasa jam'iyyar PDP ba za ta shiga zaben da za a yi ba a ranar 16 ga watan Janairun 2021.

A bangaren kudi har naira biliyan 2.3 da aka ware domin zaben, PDP ta ce ba za ta shiga cikin harkallar da aka shirya domin kwashe kudin jihar Kano ba.

A wani labari na daban, malaman addinin musulunci sun hassala da mulkin Shugaba Muhammadu Buhari sakamakon yadda harkokin tsaro kullum suke kara tabarbarewa a Najeriya, musamman yankin arewa.

Malamai da dama sun caccaki gwamnatin Shugaba Buhari, wanda har suke nuna cewa sun dawo daga rakiyarsa.

Sun bayyana ra'ayoyinsu ne a tattaunawar da BBC tayi da su, inda suke nuna yadda Allah zai yi fushi da gwamnatin Shugaba Buhari matsawar bai shawo kan matsalar tsaro ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel