Ina cikin tashin hankali a jihata, kiranmu kadai ake da shugabannin tsaro, El-Rufai (Bidiyo)

Ina cikin tashin hankali a jihata, kiranmu kadai ake da shugabannin tsaro, El-Rufai (Bidiyo)

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana damuwarsa a kan rashin ikonsa da 'yan sanda

- A cewarsa, ana kiran shi da takwarorinsa shugabannin jami'an tsaro ne a baki kawai

- Amma a zahiri, basu da ta cewa a kansu, sifeta janar na 'yan sanda ne kadai yake bayar da umarni

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana damuwarsa a kan rashin damar bayar da umarni ga 'yan sanda a kan kashe-kashe da tabarbarewar tsaro a Najeriya.

A wata tattaunawa da gidan talabijin din Channels suka yi da gwamnan a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba, El-Rufai ya bayyana damuwar da shi da takwarorinsa na sauran jihohi suka shiga a kan harkokin tsaron kasar nan.

Gwamnan ya ce ana kiran gwamnoni da shugabannin jami'an tsaro ne a baki kawai, amma a zahiri, basu da damar tankwara 'yan sanda.

KU KARANTA: Da duminsa: ISWAP sun yi awon gaba da jami'an gwamnatin Borno 3 a Damasak

Ina cikin tashin hankali a jihata, kiranmu kadai ake da shugabannin tsaro, El-Rufai (Bidiyo)
Ina cikin tashin hankali a jihata, kiranmu kadai ake da shugabannin tsaro, El-Rufai (Bidiyo). Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke wani mutum da ake zargi da safarar makamai da harsasai 299

Ya ce ba shi da damar neman 'yan sandan da za a tura jiharsa zuwa ga kwamishinan 'yan sandan jiharshi, da kuma bayar da umarni a kan harkokin 'yan sanda har sai Sifeta Janar ya yarda kuma ya bayar da umarni tukunna.

A wani labari na daban, a ranar Litinin, rundunar sojin Najeriya ta nuna takaicin yadda wasu 'yan arewa maso gabas suke kin bai wa jami'an tsaro bayanai wadanda za su taimaka wurin bincike.

A kalla manoma 43 ake zargin 'yan Boko Haram sun kashe a Zabarmari, jihar Borno a ranar Asabar, Channels TV ta ruwaito.

UN ta ce kisan da aka yi ya kai mutane 110. Sannan wannan harin da aka kai na kwanan nan ya yi tsanani a cikin hare-haren arewa maso gabas da ake kaiwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel