Rade-radin sabuwar zanga-zanga: FG ta sanar da tsatsauran matakin da za ta dauka
- Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu ya ja kunnen matasan da ke shirin rikito wata zanga-zangar EndSARS
- Ya ce sam ba za su lamunci tayar da zaune tsaye ba, za su dauki tsauraran matakai a kan duk wanda ya aikata hakan
- Ya fadi hakan ne bayan jin labarin matasa suna shirin ballo wata zanga-zangar a ranar 5 ga watan Disamba
Gwamnatin tarayya za ta taka wa duk wani mai zanga-zanga a kan cutarwar dan sanda da wasu matsololi makamantan haka burki, jaridar Thisday ta wallafa haka.
Ta ce duk wanda ya gwada kawo cikas ga zaman lafiya ko kuma harkar tsaron kasa zai kwashi kashinsa a hannu.
Gwamnatin tarayya ta zargi za a fara wani sabon zanga-zanga na EndSARS a ranar 5 ga watan Disamba, wanda yake ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani.
KU KARANTA: Kisan Zabarmari: Gwamnoni 36 sun kushe lamarin, sun bayyana matakin dauka
Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu ya sanar da hakan bayan ya yi taro da kwamishinonin 'yan sandan jihohi 36 da ke fadin kasarnan a ranar Juma'a, inda yace wajibi ne jami'an tsaro su yi wa al'amarin garanbawul.
Kamar yadda matasa suka yi zanga-zanga a watan Oktoba, wanda matasan kudu da na Abuja suka rikitar da kasar gabadaya. Al'amarin ya janyo tashin hankula iri-iri, har rikicin kashe-kashen Lekki Tollgate da aka yi ranar 20 ga watan.
Rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan sanda 22 sannan har dukiyoyin gwamnati da na al'umma matasan suka lalata na tiriliyoyin nairori.
KU KARANTA: Rundunar soji ta bayyana wadanda ke wa tsaro zagon kasa a arewacin Najeriya
A wani labari na daban, hukumar 'yan sandan jihar Cross River sun damki wani mutum mai shekaru 52 mai suna Cyprain Mbe, wanda ake zargin yana safarar miyagun makamai.
An kama shi lokacin da 'yan sanda suka fita sintiri yayin da suka dakatar da ababen hawa don su bincikesu a karamar hukumar Etung da ke jihar, The Nation ta wallafa.
Ana zargin Cyprain Mbe dan kauyen Bashia da ke karamar hukumar Boki da safarar makamai. An kama shi a kwanakin karshen mako da curin alburusai guda 299 boye cikin wata bakar jaka.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng