Kisan Zabarmari: Duk malamin da bai yi huduba a kan tsaro ba munafuki ne, Malam Maraya

Kisan Zabarmari: Duk malamin da bai yi huduba a kan tsaro ba munafuki ne, Malam Maraya

- Malaman addinin musulunci sun caccaki gwamnatin Buhari a kan rashin tsaro

- A cewarsu, ya gaza kuma duk shugabannin Najeriya su ji tsoron Allah don zai tambayesu

- Sun kuma caccaki malaman da suka yi shiru a kan lamarin, da cewa watarana zai zo kansu

Malaman addinin musulunci sun hassala da mulkin Shugaba Muhammadu Buhari sakamakon yadda harkokin tsaro kullum suke kara tabarbarewa a Najeriya, musamman yankin arewa.

Malamai da dama sun caccaki gwamnatin Shugaba Buhari, wanda har suke nuna cewa sun dawo daga rakiyarsa.

Sun bayyana ra'ayoyinsu ne a tattaunawar da BBC tayi da su, inda suke nuna yadda Allah zai yi fushi da gwamnatin Shugaba Buhari matsawar bai shawo kan matsalar tsaro ba.

Wannan ya biyo bayan kisan manoman jihar Borno guda 43 da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka aiwatar.

Tsaron kasa: Malaman addini sun yi wa Buhari wankin babban bargo
Tsaron kasa: Malaman addini sun yi wa Buhari wankin babban bargo. Hoto daga @GOVBORNO
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke wani mutum da ake zargi da safarar makamai da harsasai 299

BBC ta tattauna da fitaccen Malamin nan na jihar Kano, Malam Aminu Ibrahim Daurawa, wanda ya nuna cewa wajibi ne Shugaba Buhari ya kawo karshen wannan matsalar da ta addabi arewacin Najeriya.

Kamar yadda yace, "Muna kira ga shugabanninmu da su san cewa Allah zai tambayesu a kan yadda suka tafiyar da mulkinsu, su kuma ji tsoron Allah, don suna da alhakin kula da rayuka miliyan 200."

"Su tuna da alkawuran da suka dauka, na dagewa wurin kawo karshen rashin tsaro, gyara a bangaren noma da kuma hana cin hanci da rashawa," a cewarsa.

Yace "Wadannan abubuwa su ne suka taru suka addabi Najeriya, don haka ya kamata shugaba Buhari ya shawo kansu."

KU KARANTA: Kisan manoma 40: Duniya bata siyarwa da Najeriya makamai, an bar mu hannun 'yan ta'adda, Lai Mohammed

Bayan an tattauna da Malam Halliru Maraya, ya bayyanar da yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya gaza da mulkin Najeriya.

Ya ce gwamnati ta kasa aiwatar da ayyuka yadda ya kamata. Da kuma kula da rayuka da dukiyoyin al'umma, yanzu haka komai ya kazanta.

Da aka tattauna da Malam Musa Yusuf, wanda ake kira Asadus-Sunnah, ya caccaki malaman da suka zura ido suna kallon yadda harkokin tsaro suka tabarbare a Najeriya kuma suka yi shiru.

A cewarsa, "Duk malamin da yayi hudubar ranar Juma'a ba tare da ya sanya maganar tabarbarewar tsaro ba, ya ci amanar addinin musulunci."

Ya ce bai dace a ce ana kashe musulman Najeriya ba, kuma mutum ya tattauna a kan wani maudu'in daban ba. Ya ce lallai ya kamata malamai su bude baki su yi magana, idan ba haka ba, watarana zai zo kansu.

A wani labari na daban, labari da duminsa da ke zuwa daga jaridar HumAngle shine na sace jami'an gwamnatin jihar Borno da mayakan ta'addanci na ISWAP suka yi a ranar Litinin a Damasak.

Kamar yadda aka gano, jami'an gwamnatin suna tafiya ne a ababen hawa yayin da 'yan ta'addan suka tsare su a wani wuri da ake kira da Wakilti.

Daga nan suka iza keyarsu tare da yin garkuwa da su domin neman kudin fansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel