'Yan sandan da ya dace su yaki 'yan bindiga ne ke rike jakar matan manya, El-Rufai
- Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana damuwarsa a kan rashin tsaron da ke addabar jiharsa
- A cewarsa, 'yan sandan da yakamata a ce suna yakar 'yan ta'adda suna can suna rike jakunkunan manyan mata
- Ya bayyana bukatarsa ta canja kundin tsarin Najeriya domin bai wa jihohi damar amfana da 'yan sandansu
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya nuna takaicinsa a kan yawan 'yan sandan da ya kamata su yi yaki da ta'addanci amma suna can suna yin akasin hakan, kamar rikewa matan manyan mutane jakunkuna.
El-Rufai ya ce ya harzuka a kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa, ya kuma bayyana bukatar 'yan sanda su shiga lamarin.
Ya bukaci majalisar tarayya da ta gyara dokar bai wa jihohi damar amfana da 'yan sanda da kansu.
Gwamnan ya ce ya kamata a ce gwamnonin jihohi ne suke da alhakin kulawa da ayyukan yau da kullum na 'yan sandan jihohinsu.
KU KARANTA: Boko Haram ta taba zaben kwamishina a Borno, dan jarida ya tona asirin tushen ta'addanci
El-Rufai ya yi maganar ne a ranar Litinin da daddare a gidan talabijin din Channels, shirin da The Punch suka kula dashi.
A cewarsa, "Mun dade muna cece-kuce a kan yadda ya kamata a ce an baiwa jihohi damar amfana da 'yan sandansu.
"Sannan yawan 'yan sandan da muke da su a Najeriya ba za su wadacemu ba, ba su wuce rabin yadda muke bukata ba. Sannan a hakan da yawansu suna can suna ayyukan da ba za su amfani al'umma ba, kamar rike jakunkunan matan manyan mutane.
"Ya kamata a ce muna da 'yan sanda da yawa a Najeriya, hakan zai samu ne idan aka yi gaggawar canja kundin tsarin mulki kuma kwamitin kishin kasa na APC ya bukaci 'yan sanda, wannan zai bayar da damar kara yawan 'yan sanda.
KU KARANTA: Kisan Zabarmari: Gwamnoni 36 sun kushe lamarin, sun bayyana matakin dauka
"Idan aka bai wa jihohi damar amfana da 'yan sandansu, gwamnatin tarayya za ta dinga biyansu albashi, amma gwamnatin jiha za ta iya biyan 'yan kudaden mai na motocinsu da sauransu.
"To me muke tsoro? Mu yi gaggawar gyara kundin tsarin mulkin don gwamnatin jihohi ta fara samun damar amfana da 'yan sandan ta."
A wani labari na daban, a ranar Litinin, rundunar sojin Najeriya ta nuna takaicin yadda wasu 'yan arewa maso gabas suke kin bai wa jami'an tsaro bayanai wadanda za su taimaka wurin bincike.
A kalla manoma 43 ake zargin 'yan Boko Haram sun kashe a Zabarmari, jihar Borno a ranar Asabar, Channels TV ta ruwaito.
UN ta ce kisan da aka yi ya kai mutane 110. Sannan wannan harin da aka kai na kwanan nan ya yi tsanani a cikin hare-haren arewa maso gabas da ake kaiwa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng