Kisan manoma 40: Duniya bata siyarwa da Najeriya makamai, an bar mu hannun 'yan ta'adda, Lai Mohammed

Kisan manoma 40: Duniya bata siyarwa da Najeriya makamai, an bar mu hannun 'yan ta'adda, Lai Mohammed

- Muna bukatar taimakon kasashen ketare don kawo karshen ta'addanci, cewar ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed

- A cewarsa, akwai makamai na musamman da ya kamata Najeriya ta mallaka, idan ba haka ba, 'yan ta'adda za su cigaba da cutar da mutane

- Ministan ya fadi hakan ne lokacin da ya kai ziyara ga gwamnan Makurdi, Samuel Ortom, har yace akwai masu daukar nauyin 'yan ta'addan

Ministan Labarai da al'adu, Lai Mohammed, a ranar Litinin yace a yanzu haka an bar Najeriya da 'yan ta'adda saboda an hana ta makaman yakar 'yan ta'adda duk da kokarin da takeyi wurin yakarsu.

Ministan ya nuna alhininsa a kan kisan manoma 43 na Zabarmari, karamar hukumar Jere da ke jihar Borno, inda yace gwamnatin tarayya ba za ta zauna ba har sai ta kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Alhaji Mohammed ya yi maganar ne a Makurdi yayin da ya kaiwa gwamna Samuel Ortom ziyara, inda yace 'yan ta'addan suna samun kudade daga kasashen ketare, Vanguard ta wallafa.

KU KARANTA: Kisan Zabarmari: Ka sallami shugabannin tsaro, NAS ga Buhari

Kisan manoma 40: Duniya bata siyarwa da Najeriya makamai, an bar mu hannun 'yan ta'adda, Lai Mohammed
Kisan manoma 40: Duniya bata siyarwa da Najeriya makamai, an bar mu hannun 'yan ta'adda, Lai Mohammed. Hoto ddaga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mutum 1 ya sheka lahira yayin arangamar 'yan sanda da 'yan fashin teku

A cewarsa, "Idan mutane suna batun ta'addanci, basa ganin cewa zai iya addabar duniya gabadaya, sannan kowacce kasa tana fuskantar nata ta'addancin.

"Ba za mu dakata ba a kan kulawa da lafiya da walwalar al'umma ba, amma ya kamata jama'a su san cewa akwai masu daukar nauyin namu 'yan ta'addan kuma muna bukatar kasashen duniya su tallafa mana.

"Misali, Najeriya tana bukatar makamai masu inganci wurin yakar ta'addanci amma ya ci tura, kuma idan ba mu da isassun makamai 'yan ta'adda za su cigaba da addabarmu."

A wani labari na daban, darekta janar na PGF, Dr. Salihu Lukman, ya alakanta rikicin cikin jam'iyyar APC da dagewar wasu jiga-jigan jam'iyyar wurin gasa da juna, jaridar The Punch ta wallafa.

Ya bayyana hakan a wata takarda mai taken, "Demokradiyyar Najeriya da gasar tsayawa takara cikin jam'iyya," a Abuja ranar Lahadi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng