Da duminsa: ISWAP sun yi awon gaba da jami'an gwamnatin Borno 3 a Damasak

Da duminsa: ISWAP sun yi awon gaba da jami'an gwamnatin Borno 3 a Damasak

- Labarin da duminsa a halin yanzu shine sace wasu jami'an gwamnatin Borno da aka yi

- Jami'an uku suna tafiya ne a hanyar Wakilti da ke Damasak a karamar hukumar Mobbar

- Mayakan ta'addanci na ISWAP sun tsaresu inda suka iza keyarsu domin neman kudin fansa

Labari da duminsa da ke zuwa daga jaridar HumAngle shine na sace jami'an gwamnatin jihar Borno da mayakan ta'addanci na ISWAP suka yi a ranar Litinin a Damasak.

Kamar yadda aka gano, jami'an gwamnatin suna tafiya ne a ababen hawa yayin da 'yan ta'addan suka tsare su a wani wuri da ake kira da Wakilti.

Daga nan suka iza keyarsu tare da yin garkuwa da su domin neman kudin fansa.

Al'amuran ta'addanci yana cigaba da tsananta a yankin arewacin Najeriya, hakan kuwa yana ,matukar tada wa jama'a hankula tare da saka su yin kiraye-kiraye ga gwamnati da ta dauka mataki.

KU KARANTA: Boko Haram ta taba zaben kwamishina a Borno, dan jarida ya tona asirin tushen ta'addanci

Da duminsa: ISWAP sun yi awon gaba da jami'an gwamnatin Borno 3 a Damasak
Da duminsa: ISWAP sun yi awon gaba da jami'an gwamnatin Borno 3 a Damasak. Hoto daga @HumAngle
Source: Twitter

KU KARANTA: Baka san darajar da ka kara a idon masu caccakarka ba, Ndume ga Jonathan

A wani labari na daban, NAS ta bukaci shugaban kasa da yayi gaggawar sauke shugabannin tsaro a kan kashe manoman shinkafa 43 da 'yan Boko Haram suka yi a Zabarmari, a karamar hukumar Jere da ke jihar Borno, jaridar Vanguard ta wallafa.

Mr. Abiola Owoaje, wani jagaban NAS, ya gabatar da wata takarda mai taken "Kisan da 'yan ta'adda suka yi na manoman shinkafan Zabarmari guda 43", ya bayyana al'amarin a matsayin abu mai razanarwa da tsoratarwa.

A cewarsa, "Wannan kisan a cikin kashe-kashen da aka yi ta yi marasa iyaka musamman a arewa maso gabas da sauran yankuna a Najeriya, yana nuna mummunan tsarin harkar tsaron Najeriya tun daga farko."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel