Korafi: Pantami ya dauki alkawarin isar da sakon 'yan arewa ga Buhari

Korafi: Pantami ya dauki alkawarin isar da sakon 'yan arewa ga Buhari

- Batun kisan manoma 43, da mayakan kungiyar Boko Haram suka yanka, ya tayar da hankulan jama'a

- Jama'a da dama, musamman 'yan arewa, sun mamaye dandalin sada zumunta da alhinin kisan manoman

- Wasu ma'abota amfani da dandalin sada zumunta na tuwita sun roki ministan sadarwa, Dakta Isa Pantami, ya isar da sakonsu ga Buhari

Dakta Isa Pantami, ministan Sadarwa da tattalin arziƙin fasahar yanar gizo, ya ce zai miƙa saƙonnin jama'a ga Shugaban ƙasa Muhammad Buhari bisa kisan gillar da ƴan Boko Haram suka yi na manoma 43.

A jiya, asabar, ne rahotanni suka bayyana cewa ƴan Boko Haram sun shiga ƙauyen Zabarmari, dake ƙaramar hukumar Jere, jihar Borno, sun bi manoma har gonakinsu sun yi musu yankan rago.

Sheik Pantami ya bayyana hakan ne a shafinsa na sadarwarsa a manhajar Tuwita bayan wani mai amfani da shafin ya roƙe shi da yin hakan.

KARANTA: Sunayensu: PDP ta kafa kwamitin mutane 6 domin fara zawarcin gwamnonin APC

Wanda yayi roƙon mai suna Boss Mustapha@__yellows) ya rubuta kamar haka.

Zan kai saƙonƙu ga shugaba Kan ƴan ta'adda Boko Haram
Korafi: Pantami ya dauki alkawarin isar da sakon 'yan arewa ga Buhari @Thecable
Asali: Twitter

"Ya Sheikh @DrIsaPantami - muna kawo kukan mu gareka. Dan Allah dan Annabi ka samu ka yi ma shugaban qasa magana. Mutum arba’in da uku (43), ko a fim aka kashe wannan adadi lokaci daya, abun zai bada tsoro.

"Dan Allah a taimaka a yi wani abun a kai, abun ya fara yawa

#ZabarmariMassacre".

KARANTA: Bauchi: An yi ram da Sadiya Kaura, matashiyar da ke bawa 'yan fashi da barayi mafaka

Shi kuma Pantami sai ya mayar masa da martani cikin harshen turanci kamar haka.

"Muna ta yin hakan, kuma zamu cigaba da yin hakan In sha Allah.

"Shi ma zan yi masa magana kamar yadda nayi magana da gwamna Zulum ɗazun nan.

"Allah ya jiƙansu, ya kuma kawo mana ƙarshen wannan bala'in"

Arewacin Najeriya dai na fama da matsanancin matsalar rashin tsaro da ta haɗar da Boko Haram, ƴan bindiga daɗi, ƴan fashin daji da masu garkuwa da mutane.

Rahotanni daga ƙididdigar baya bayan nan sun nuna cewa an yi garkuwa da fiye da mutane 1,500 a arewacin Najeriya baya ga biyan ɗimbin kuɗaɗen fansa.

Kazalika, rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutane 36,000 rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar rasa rayukansu tun daga shekarar 2009, da ƙungiyar ta ɓulla, zuwa yanzu.

Kazalika ayyukan ƙungiyar sun tilastawa sama da mutum miliyan biyu barin muhallansu, inda ƴan Najeriya 240,000 suka yi gudun hijira zuwa maƙwabtan ƙasashe.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa fashewar wasu sinadarai da ake ke zargin bama-bamai ne a Cocin mahaifin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya girgiza jama'a a wani bangare na birnin Fatakwal.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel