'Yansanda sun yi ram da wata mata mai bawa ƴanfashi, ɓarayi da masu laifi mafaka
- Rundunar 'yan sanda a jihar Bauchi ta yi caraf da wata mata mai suna Sadiya Yaro bisa zarginta da bawa batagari mafaka
- Kakakin 'yan sandan jihare Bauchi, DSP Mohammed Ahmed Wakili, ya ce matare ta nadi muryarta tana yabon 'yan ta'adda
- Ya ce an kama wasu 'yan daba a gidanta tun bayan tserewarsu daga hannun hukuma a shekarar 2019
Ƴan sandan jihar Bauchi sun kama wata mata da ake zargi da bawa masu muggan laifuka mafaka sakamakon kama ɓarayi biyu da ƴan fashi a gidanta.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, DSP Mohammed Ahmed Wakili, shine ya bayyana hakan ranar a Alhamis.
Ya ce jami'an rundunar, bayan samun bayanan sirri, sun kama wata Sadiya Mohammed Yaro wacce aka fi sani da Sadiya Ƙaura, ƴar shekara 28, a unguwar ƙofar Dumi ta garin Bauchi.
KARANTA: Nyesom Wike: Buhari zai cinnawa Najeriya wuta idan ya ƙi biyan buƙatun jama'a
Acewarsa, matar ta bawa masu laifi mafaka a gidanta dake ƙofar Ɗumi jim kaɗan bayan sun kai hari ofishin Komiti a garin Bauchi.
An ji matar ta naɗi muryarta tana kirari da yabon ƴan daban, tana mai goyon ɓayansu.
Wakili ya ce ƴansanda sun kama masu laifi biyu masu suna; Yakubu Hussaini wanda aka fi sani da Abba Laba, mai shekaru 20.
KARANTA: Tabarbarewar tsaro: Nigeria ta zama kasa ta uku mafi shahara a ta'addanci a duniya
Sai kuma Bashir Ahmad wanda aka fi sani da Bashoo, mai shekaru 23, dukkansu daga ƙofar Ɗumi, kuma suna cikin sanannu ƴan daban da suka addabi jihohin Bauchi, Gombe, Plateau da Kaduna.
Ya ce ƴan ta'addan sun tsere daga hannun hukuma a shekar 2019.
Ya kara da cewa suna daga cikin waɗanda suka kai harin Ofishin kwamiti a unguwannin Zango da Ƙofar Ɗumi a jihar Bauchi.
Za'a shigar da laifunsu sannan a gurfanar da su a gaban kuliya su girbi abin da shuka, a cewarsa.
Legit.ng Hausa ta rawaito Dakta Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Delta, na yin kira ga 'yan Najeriya da su mika al'amuransu ga Allah.
A cewar gwamna Okowa, alhakin jama'a ne su ririta rayuwarsu saboda al'amura sun rincabe a Nigeria.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng