'Yan ta'adda sun tashi sinadarai masu fashewa a Cocin mahaifin gwamna Wike

'Yan ta'adda sun tashi sinadarai masu fashewa a Cocin mahaifin gwamna Wike

- Wasu 'yan ta'adda sun saci numfashin mutane sun shiga Cocin da mahaifin gwamna Wike na jihar Ribas ke halarta

- 'Yan ta'addar, su biyar, sun dasa tare da tashin sinadarai masu fashewa da aka hada da sinadarin 'Dynamite'

- A cikin makon da ya gabata ne gwamna Wike ya sanar da shugaba Buhari cewa zai cinnawa Nigeria wuta idan ya gaza biyan bukatun jama'a

Fashewar wasu sinadarai da ake ke zargin bama-bamai ne a Cocin mahaifin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya girgiza jama'a.

The Nation ta rawaito cewa wasu 'yan ta'adda ne, su biyar, suka samama zuwa cikin Cocin a daren ranar Asabar tare da dasa sinadaran da kuma tashinsu.

Tashin sinadaran masu fashewa ya lalata mafi yawan ginin Cocin mai suna 'Christian Universal International Church', wacce aka gina a fili mai lamba 25 da ke kan titin Azikiwe, Mile 3, a garin Fatakwal.

Karar fashewar sinadaran ta jefa mazauna yankin cikin fargaba da zama dar-dar.

KU KARANTA KUMA: An gano Ndume tare da Jonathan yan kwanaki bayan sakinsa daga kurkukun Kuje

Duk da babu wata kungiya da ta fito ta bayyana daukan alhakin kai hari Cocin, 'yan bijilanti sun kama wasu batagari guda biyu da ake zargin suna daga cikin wadanda suka kai harin.

Tuni 'yan bijilanti suka damka batagarin da suka kama a hannun rundunar 'yan sanda.

Jami'an rundunar atisayen 'Eagle Crack' ta rundunar 'yan sanda da sauran jami'an hukumomin tsaro sun kewaye harabar Cocin da yankin da abin ya faru, Kamar yadda The Nation ta rawaito.

'Yan ta'adda sun tashi sinadarai masu fashewa a Cocin mahaifin gwamna Wike
'Yan ta'adda sun tashi sinadarai masu fashewa a Cocin mahaifin gwamna Wike Hoto: @GuardianNigeria
Source: Facebook

KU KARANTA KUMA: Da sauran rina a kaba: ASUU ta yi karin haske a kan rahotannin janye yajin aiki

A cikin makon da ya gabata ne gwamna Wike ya yi gargadin cewa shugaba Buhari zai cinnawa Nigeria wuta idan ya gaza biyan bukatun jama'a.

Gwamnan ya fadi hakan ne yayin wani taro na musamman da wakilan fadar shugaban kasa suka yi da gwamnoni da jagororin al'ummar yankin kudu maso kudu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel