PDP ta kafa kwamitin mutane 6 domin fara zawarcin gwamnonin APC

PDP ta kafa kwamitin mutane 6 domin fara zawarcin gwamnonin APC

- Jam'iyyar adawa, PDP, ta yi rashin wasu manyan mambobinta da suka sauyab sheka zuwa jam'iyyar APC a cikin watan nan

- Daga cikin wadanda suka sauya sheka daga PDP zuwa APC akwai gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi

- Domin mayar da martani a kan dauki dai-dai da jam'iyyar APC ke yi wa mambobinta, PDP ta kafa kwamitin daukan ramuwar gayya

Babbar Jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta kafa wani kwamiti na mutane 6 da zai fara zawarcin gwamnoni da mambobin majalisa na jam'iyyar APC, kamar yadda jaridar Punch ta ranar Lahadi ta wallafa.

Punch ta bayyana cewa PDP ta kafa kwamitin ne a matsayin martani ga sauyin sheka da wasu manyan mambobinta, da suka hada da gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi, suka yi zuwa APC.

Tsohon shugaban majalisar dattijai kuma tsohon dan takarar kujerar shugaban kasa, Bukola Saraki, ne jagoran kwamitin mutane 6 da PDP ta kafa.

KARANTA: An dawowa da Nigeria gunkin Ife Terracotta mai shekaru 600 daga kasar Netherlands

Sauran mambobin kwamitin sun hada da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Sanata Anyim Pius Anyim, tsohon gwamna a jihar Kuros Riba, Liyel Imoke, da tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema.

PDP ta kafa kwamitin mutane 6 domin fara zawarcin gwamnonin APC
PDP ta kafa kwamitin mutane 6 domin fara zawarcin gwamnonin APC
Source: Twitter

Sauran sun hada da tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, da tsohuwar shugabar marasa rinjaye a majalisar wakilai, Mulikat Akande.

Sakataren yada labaran jam'iyyar PDP, Bola Ologbondiyan, ne ya sanar da hakan a cikin wani sako da ya wallafa a shafin jam'iyyar PDP da ke kan manhajar tuwita.

KARANTA: An yi ram da Sadiya Kaura, matashiya mai bawa ƴanfashi da ɓarayi da masu laifi mafaka

Sai dai, Punch ta wallafa cewa wata majiya daga cikin jam'iyyar PDP ta sanar da ita cewa an umarci Saraki da sauran mambobin kwamitinsa su shiga zawarcin manyan mambobin jam'iyyar APC mai mulki.

A makon da ya kare ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe, ya ce "Jam'iyyar APC nan bada jimawa ba za ta jijjiga siyasar Najeriya da al-ajabin da ba'a taɓa samun irinsa ba a ƙasar"

Jam'iyyar APC zata fuskanci karɓar mutane masu sauya sheƙa daga jam'iyyu mabambanta zuwa APC a satattuka masu zuwa, a cewar Mai Mala Buni.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel