Matawalle ya jinjina yiwuwar barin PDP, ya ce 'Ina fuskantar matsaloli; na yi wa Umahi murna'

Matawalle ya jinjina yiwuwar barin PDP, ya ce 'Ina fuskantar matsaloli; na yi wa Umahi murna'

- Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya taya Dave Umahi na jihar Ebonyi murnar ficewa daga jam'iyyar PDP

- Matawalle ya bayyana cewa akwai wasu matsaloli a jam'iyyar ta PDP wadda sune sukayi sanadin Umahi ya fice daga jam'iyyar

- Matawalle ya ce bai ga laifin Umahi ba don idan ba a maraba da mutum a wuri ba zai iya cigaba da zama ba

- Gwamnan Zamfarar ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda gwamnonin kudu maso kudu suka shiga kafafen watsa labarai suna yada karya kan gwal din Zamfara

Gwamman Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya yabawa takwararsa na Jihar Ebonyi, David Umahi da ya fice daga jam'iyyar PDP ya koma APC.

Mista Matawalle ya alakanta ficewar Mista Umahi daga PDP ta "rashin jituwa tsakanin mambobin jamiyyar ta Peoples Democratic Party”.

Gwamnan Zamfaran, wanda dan jam'iyyar PDP ne ya yi wannan jawabin ne ta bakin mai magana da yawunsa, Zailani Bappa a ranar Juma'a kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Matawalle ya jinjina yiwuwar barin PDP, ya ce 'Ina fuskantar matsaloli; na yi wa Umahi murna'
Matawalle ya jinjina yiwuwar barin PDP, ya ce 'Ina fuskantar matsaloli; na yi wa Umahi murna'. Hoto: @daily_nigerian
Asali: UGC

Mista Matwalle ya ce ya gwammace ya jinjinawa Mista Umahi "kan babban matakin da ya dauka a maimakon sukarsa domin mutum na iya zama ne a gidan da ake maraba da shi."

DUBA WANNAN: Kotu ta yanke wa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa hukuncin shekaru 3 a gidan maza

"Idan wannan rashin jituwar ya cigaba da wanzuwa ba a magance shi ba, jam'iyyar mu ce za ta cigaba da fuskantar matsala a yayin da muke tunkarar zaben 2023," a cewar Gwamna Matawalle.

"Ina fuskantar kallubalai a baya-bayan nan daga wasu takwarorina na PDP kuma hakan na daure min kai. Misali, gwamnonin PDP na Kudu maso Kudu sun shiga kafafen watsa labarai suna ruruta wutar batun gwal din Zamfara bisa rashin fahimta da karerayi," inji Gwamna Matawalle.

"Abin mamaki, gwamnatin tarayya ta APC ce ta fito ta bayyana gaskitar lamarin kan hakkar gwal din ta kare ni a kan batun. A matsayinsu na 'yan uwana na PDP, ina tsammanin zasu tuntube ni don jin ta baki na kafin su fara yada maganganu marasa dadi a kafafen watsa labarai," in ji shi.

Gwamna Matawalle ya yabawa gwamnatin tarayyar Najeriya da Shugaba Muhammadu Buhari bisa goyon bayansa wurin tsara bangaren tattalin arzikin jiharsa don kare amfani da ma'adinan wurin janyo fitintinu a jihar.

KU KARANTA: Hotuna: Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kwato makamai da alburusai da dama

"A yau gwamnatin tarayya tarayya tana bada lasisi ga kamfanonin suka cancanta a jihar. Kamfanin data saka hannun jari mafi girma mallakin wani dan Najeriya ne daga jihar Anambra. A yanzu, gwamnatin jiha bata da hannu a harkar hakar ma'adinai don kudin tsarin mulki bai bamu dama ba.

"Ina kira ga gwamnonin kudu maso kudu su kauracewa lalaci su tallafawa mutanensu su bude kananan matattun man fetur kamar yadda doka ta basu iko a maimakon yada jita-jita," in ji Matawalle.

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya, Sanata Joseph Wayas, yana wata asibiti a birnin Landan sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Wayas shine shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu daga shekarar 1979 zuwa 1983 a lokacin da marigayi Alhaji Shehu Shagari ke shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel