Tsohon shugaban majalisa, Joseph Wayas, yana kwance rai a hannun Allah a Landan

Tsohon shugaban majalisa, Joseph Wayas, yana kwance rai a hannun Allah a Landan

- Tsohon shugaban majalisar dattawa, Joseph Wayas, yana kwance a asibiti rai a hannun Allah a Landan

- Sanata Joseph Wayas ya shugabanci majalisar dattawar Najeriya a jamhuriya ta biyu daga 1979 zuwa 1983

- Gwamnatin Jihar Cross Rivers ce ta dauki dawainiyar yi masa magani kamar yadda gwamnan jihar Ben Ayade ya umurta

Tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya, Sanata Joseph Wayas, yana wata asibiti a birnin Landan sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wayas shine shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu daga shekarar 1979 zuwa 1983 a lokacin da marigayi Alhaji Shehu Shagari ke shugaban kasa.

Tsohon shugaban majalisar, Joseph Wayas, yana kwance rai a hannun Allah a Landan
Tsohon shugaban majalisar, Joseph Wayas. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Iyalan mai tallar jarida da aka kashe sun nemi naira miliyan 500 daga wurin kakakin majalisa

An dade ba a ga Wayas ba a cikin mutane a shekarun baya bayan nan.

Gwamna Ben Ayade na Jihar Cross River wanda ya tabbatar da rashin lafiyar tsohon shugaban majalisar ya ce jihar zata dauki nauyin yi wa dattijon kasar magani.

Ayade ya umurci kwamishinan lafiya na jihar Cross River, Dakta Betta Edu da tawagarta su tafi da shi Landan nan take kuma su cigaba da sa ido kan kulawar da ake bashi.

KU KARANTA: Yan bindiga sun afka wasu kauyukan uku a Zamfara, sun kashe uku, mazauna gari sun tsere

Gwamnan cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Christian Ita, hadiminsa na bangaren watsa labarai ya ce: "Jihar ba zata yi kasa a gwiwa ba wurin kashe kudi don ganin an samarwa tsohon shugaban majalisar lafiya."

A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel