Maina: Kotu ta tsayar da ranar Juma’a don yanke hukunci kan bukatar belin Ndume

Maina: Kotu ta tsayar da ranar Juma’a don yanke hukunci kan bukatar belin Ndume

- Alkalin babbar kotun tarayya ta Abuja, Okon Abang ya tsayar da ranar Juma'a don yanke hukunci kan bukatar belin Ndume

- Abang dai ya tsare Ndume a gidan maza tun ranar Litinin bayan ya kasa gabatar da Abdulrasheed Maina a gabansa

- Sanatan shine ya tsayawa tsohon shugaban na hukumar fansho a matsayin jingina a shari'arsa da EFCC

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tsayar da ranar Juma’a, 27 ga watan Nuwamba, domin zartar da hukunci a kan bukatar bayar da belin Sanata mai wakiltan Borno ta Kudu, Ali Ndume, Channels TV ta ruwaito.

An dai tsare Ndume a gidan yarin Kuje tun a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba, kan tsayawa Abdulrasheed Maina da yayi a matsayin jingina inda shi kuma ya tsere.

Justis Okon Abang a ranar Alhamis, ya dage zaman yanke hukuncin bayan lauyan Sanata Ndume, Marcel Oru, ya yi muhawara kan bukatar belin, inda shi kuma lauyan hukumar yaki da rashawa, Mohammed Abubakar ya nuna adawa.

Maina: Kotu tsayar da ranar Juma’a don yanke hukunci kan bukatar belin Ndume
Maina: Kotu tsayar da ranar Juma’a don yanke hukunci kan bukatar belin Ndume Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Maina, wanda ya kasance tsohon shugaban hukumar fansho na fuskantar shari’a kan wasu tuhume-tuhume na zambar kudade har naira biliyan biyu da EFCC ke yi masa.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta bayyana wani fitacce da suka hada kai da Maina wurin wawure kudin fansho

Justis Abang ya soke belin da aka ba Maina a ranar 18 ga watan Nuwamban 2020, sannan yayi izinin kama shi, da kuma umurnin ci gaba da shari’a a bayan idonsa.

Alkalin ya kuma tsare Sanata Ndume a gidan maza har sai ya gabatar da Maina ko kuma ya biya kudi naira miliyan 500 na yarjejeniyar belin zuwa asusun tarayya.

A ranar Talata ne Ndume ta hannun lauyansa, ya daukaka kara a kan umurnin tsare shi a gaban kotun daukaka kara, tare da takardar neman a bayar da belinsa a gaban Abang.

KU KARANTA KUMA: Mutum ne mai mutunci, Shugaban bankin AfDB Adesina ya kare Gowon kan zargin sata

A baya, mun ji cewa an hana sanatoci damar ganin Ndume a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja.

An garkame shi a ranar Litinin saboda rashin samun damar bayyana tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, wanda ya tsaya wa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel