EFCC ta bayyana wani fitacce da suka hada kai da Maina wurin wawure kudin fansho
- Wata Rouqquaya Ibrahim ta shaida wa babbar kotun tarayya cewa ba Maina kadai bane ya saci kudin fansho
- Bincike ya nuna Maina da wani ma'aikacin hukumar, Stephen Oronsaye ne suka saci naira biliyan 14 cikin kudin fansho
- Sun bude asusun bankuna fiye da 60 ba tare da amincewar akawu janar ba, suna kwasar kudade suna diddilasu ciki
Wata shaida ta ce Abdulrasheed Maina, tsohon Shugaban hukumar fansho, ya saci naira biliyan 14 cikin kudin fansho tare da wani tsohon ma'aikacin hukumar.
Rouqquaya Ibrahim ta sanar da babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa Maina da Stephen Oronsaye, wanda shine shugaban ma'aikata tsakanin 2009 zuwa 2010, sun saci kudi kimanin naira biliyan 14 sun yita zuba wa a asusun bankuna fiye da 60.
Dama EFCC ta maka karar Maina a kan zargin satar naira biliyan 2, jaridar The Cable ta ruwaito.
Alkali mai shari'a, Okon Abang, ya umarci cigaba da shari'ar bayan kin zuwan Maina kotu tun bayan bayar da belinsa.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata tare da dan na hannun daman Atiku Abubakar
A ranar Laraba, Ibrahim, shaida ta 9, wacce take daya daga cikin masu binciken EFCC, ta ce a bisa binciken da tayi, ta kama Abdulrasheed Maina da laifin satar kudin fansho mai yawa.
Kamar yadda shaidar tace, bincike ya bayyana yadda Maina yayita kwasar kudaden fansho yana diddilawa a asusun bankuna fiye da 60 wadanda Oronsaye ya bude.
Tace ofishin akawun gwamnatin tarayya ya tabbatar da babu amincewarsu wurin bude asusun ta ofishin Stephen aka budesu. Ta bude asusun bankuna 66 ba tare da amincewa ba.
KU KARANTA: Katsina: Masari ya dauka malaman makaranta 4,250 don inganta ilimi
"Bincike ya tabbatar da yadda Stephen Oronsaye yayi ta bude asusun bankuna 66, wanda su ka yi ta amfani dasu wurin satar kudaden fansho suna zubawa a cikinsu, akalla kudaden sun kai naira biliyan 14," tace.
A wani labari na daban, rundunar Operation Fire Ball ta arewa maso gabas ta ragargaji 'yan bindiga 23, sannan ta kwashe wani abu mai fashewa a hannunsu, wuraren Ngamdu, kusa da Maiduguri.
Mukaddashin jami'in hulda da jama'a, Birgediya janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan a ranar Talata, inda yace wasu daga cikin 'yan bindigan sun sha ragargaza yayin kokarin amsar kudaden fansa daga hannun iyalan wadanda aka yi garkuwa dasu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng